
Najeriya da Ghana sun sake jaddada aniyarsu ta karfafa dangantaka tsakaninsu da kuma binciko sabbin fannonin hadin gwiwa biyo bayan amincewa da sabon Babban Kwamishinan Najeriya a Ghana Jakada Shehu Ilu Barde.
Jakada Barde ya mika takardun shaidar aikinsa ga Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama a fadar Jubilee House da ke Accra inda ya zama Babban Kwamishina na 16 na Tarayyar Najeriya a kasar Ghana a hukumance.
KARANTA KUMA: Najeriya da Ghana sun karfafa dangantaka domin yaki da kyamar baki
Ma’aikatar Harkokin Waje ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta Oluwafemi Adeniyi ya sanya wa hannu.

A yayin bikin, Jakada Barde ya isar da gaisuwa mai cike da kauna da fatan alheri daga Shugaba Bola Tinubu zuwa ga Shugaba Mahama da gwamnatin Ghana da kuma al’ummar kasar.



