Wasanni

Botswana Ta Yi Kunnen Doki 1-1 Da Uganda A Wasan Neman Cancantar Shiga Gasar AFCON Ta 2027

Botswana ta yi kokarin ramawa har ta samu kunnen doki na 1-1 a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) ta TotalEnergies ta 2027 (wadda za a yi a kasashe da dama) inda ta hana Uganda daya daga cikin kasashen da za su karbi bakuncin gasar samun nasara ta biyu a Rukuni na H (Group H).

Jude Bogere ne ya fara sanya kungiyar Uganda (The Cranes) a gaba a minti na takwas amma Losika Ratshukudu ya farke kwallon a madadin Botswana a minti na 31 wanda hakan ya sa kungiyoyin biyu suka tashi kunnen doki bayan fafatawa mai zafi.

Wannan sakamakon ya sa Uganda ta ci gaba da zama a saman teburin Rukuni na H da maki biyar daga wasanni uku tana gaba da Libya da maki daya yayin da Botswana ke matsayi na uku da maki uku bayan ta yi kunnen doki a dukkan wasanninta uku da ta buga a jere.

Tunisia tana matsayi na hudu da maki biyu lamarin da ya sa gasar a rukunin ta kasance mai matukar zafi da gasa yayin da ake shiga tsakiyar matakin neman cancantar.

Karanta Kuma: Najeriya Ta Doke Tanzania Da Ci 3-1 Ta Farfado Da Fatan Samun Tikitin Shiga AFCON 2027

Wasannin Neman Cancantar AFCON: Senegal Da Côte d’Ivoire Sun Samu Nasarori Masu Muhimmanci

Uganda wacce za ta karbi bakuncin gasar ta 2027 tare da Kenya da Tanzania tuni ta samu tikitin shiga gasar kai tsaye. Hakan na nufin cewa fafatawar neman sauran tikitin da ya rage a rukunin tana da matukar muhimmanci ga Libya Botswana da Tunisia.

Wannan kunnen doki ya sa Uganda ta ci gaba da rike tarihinta na rashin shan kashi a wasannin neman cancantar wanda ya kai wasanni uku yanzu duk da cewa a yanzu ta yi kunnen doki sau biyu.

Kungiyoyin biyu za su sake haduwa a Botswana a ranar Talata 17 ga watan Nuwamba a wani muhimmin wasa da zai iya tantance makomar neman tikitin shiga gasar.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button