Kungiyar ‘Yan Jarida NUJ Reshen Gidan Radiyon Muryar Nigeria Ta Kaddamar Da Gidauniyar Naira Miliyan 34
By Hafsat Sadiq Salisu

Kungiyar Yan jarida ta Najeriya NUJ Reshen VON Ta Kaddamar Da Gidauniyar Naira Miliyan 34.
Gidauniyar zata bada damar samar da Motar mai daukar fasinjoji goma sha takwas da nufin inganta walwala da saukaka zirga zirga ga mabobinta.
Gidauniyar na daga cikin jerin shirye shiryen da kungiyar NUJ reshen VON ta shirya gudanarwa a cikin manhajanta na shirye shiryen bukin makon ‘yan Jaridu na wannan shekarar ta 2026 a Abuja.
Wannan dai shi ne karon farko bayan shekaru goma sha biyar da shugabancin wannan kungiya ta ‘yan jaridu reshen gidan rediyon Muryar Najeriya ta Kaddamar da wani ayyukan cigaba da ya jibanci mambobin ta har abokan aiki na ciki da wajen gidan su ka sheda.
Kungiyar NUJ ta fara gudanar da makon ‘yan jaridun na bana da wasannin motsa jiki da ya kunshi Tattaki na tsawon kilomita biyu da wasan Kwallon kafa tsakanin mambobinta da baki da kuma sauran nauikan wasannin motsa jiki a ranar asabar dinda ta gabata.
Yayin da a ranar Talatar da ta gabata nan kuma aka gudanar da taron lacca na karawa juna sani kan makamar aiki mai taken ” Gaskiya a zamanin kirkirarriyar basira: Aikin jarida da Dimokiradiyya da zaben shekara ta 2027″.
Farfesa Abiodun Adeniyi shugaban jami’ar Baze shi ne ya gabatar da mukala kan batun kuma aka tattauana akai domin inganta gudunar da ayyukan jarida mai inganci a wannan zamani na amafani da kirkirariyar basira da ke cike da kalubale.
A ranar alhamis Mai Zuwa za a gudanar da gwaji da binciken lafiya kyauta ga mambobin kungiyar daga wasu kwarrun likitoci da kungiyar ta gayyato.
Hafsat Sadiq Salisu.



