Hukumar Kula Da Gidajen Yari Ta Najeriya Ta Tabbatar Da Tserewar Fursunoni Biyu

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Halaye ta Najeriya (NCoS) ta tabbatar da cewa fursunoni biyu sun tsere daga Cibiyar Tsare Mutane mai Matsakaicin Tsaro da ke Okene a Jihar Kogi a ranar Lahadi 8 ga watan Nuwamba, 2026.
A cikin wata sanarwa da Jami’ar Hulda da Jama’a ta Hukumar Jane Osuji ta fitar hukumar ta bayyana cewa ta fara daukar matakan da suka dace tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro da abin ya shafa domin tabbatar da cewa an sake kama fursunonin da suka tsere din cikin gaggawa.
A halin yanzu ana jiran cikakken rahoto game da lamarin domin gano yadda tserewar ta faru. Babban Kwanturola na Hukumar ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin domin gano duk wata gazawa da ta faru da kuma daukar matakan da suka dace.
KARANTA KUMA: NCoS ta dauki tsauraran matakai kan amfani da kayayyakin da aka haramta a gidajen gyaran halaye
Hukumar ta bai wa jama’a tabbacin cewa tana ba da kulawar da ta dace kan lamarin kuma tana daukar dukkan matakan da suka dace domin sake kama fursunonin da suka tsere din.
Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Halaye ta Najeriya za ta ci gaba da bayar da karin bayani da zarar ta samu ingantattun bayanai.
Hukumar tana godiya ga jama’a bisa fahimta da hadin kan da suke bayarwa.
Aisha.Yahaya, Lagos



