NajeriyaSiyasa

Mataimakin Shugaban Kasa Shettima Ya Isa Jihar Ebonyi

Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ya isa Abakaliki babban birnin jihar Ebonyi domin kai ziyara. Jirgin dauke da Mataimakin Shugaban kasar ya sauka a Filin Jirgin Sama na Kasa da Kasa na Muhammadu Buhari da ke Abakaliki da misalin karfe 09:50 na agogon GMT.

Gwamnan jihar Francis Nwifuru ne ya tarbe shi tare da Gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma da kuma takwaransa na jihar Enugu Peter Mba.

Mataimakin Shugaban kasa Shettima ya isa jihar ne domin halartar taron yakin neman zaben jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Daga cikin manyan mutanen da ake sa ran halartar babban taron akwai Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas Shugaban jam’iyyar APC na kasa Farfesa Nentawe Yilwatda da Gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC tare da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar.

 

 

Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button