Afirka

Masu hijira 21 Sun Mutu Bayan Jirgin Ruwan Ya Nutse A Gabar Tekun Senegal

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Senegal ta ce akalla mutane 21 ne suka mutu bayan da wani kwale-kwale dauke da bakin haure da ‘yan gudun hijira ya nutse a gabar tekun arewa maso yammacin kasar inda aka ceto mutum daya da ya tsira kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi ma’aikatar ta ce an gano gawawwaki 21 kuma an ceto mutum daya tana mai bayyana adadin wadanda suka mutu a matsayin na wucin gadi har zuwa karshen Asabar.

Ta ce ana ci gaba da neman kuma ana bayar da taimako ga iyalan wadanda abin ya shafa.

KARANTA KUMA: ‘Yan cirani 139 Sun Mutu A Kifewar Kwale-kwale a gabar Djibouti

Lamarin ya kara dagula hadarin da bakin haure ke fuskanta wajen kokarin isa Tsibirin Canary na Spain ta hanyar teku daga Yammacin Afirka.

A cewar kungiyar kare hakkin ‘yan cirani Walking Borders mutane 635 ne suka mutu yayin da suke kokarin ketarewa a cikin watanni biyar na farko a shekara.

A halin yanzu hukumomi a Tsibirin Canary na El Hierro na Spain sun ayyana dokar ta-baci a ranar Asabar da ta gabata bayan karuwar masu shigowa da kwale-kwalen bakin haur Hukumomin tsibirin sun ce sama da mutane 3,300 ne suka isa cikin jiragen ruwa kimanin 30 tun farkon watan Nuwamba.

 

 

Al Jazeera/Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button