Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Yi Addu’ar Samun Hadin Kai Da Wadata Ga Najeriya A Birnin Makkah

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi addu’ar neman zaman lafiya da ci gaban Najeriya inda ya roki Allah ya sanya bambance-bambancen da ke cikin kasar su zama tushen samun wadata da ci gaba ga kasa baki daya.

Shugaban ya yi wadannan addu’o’i ne a ranar Lahadi yayin wani liyafar cin abinci a birnin Makkah na kasar Saudiyya wanda ya samu halartar gwamnonin jihohi, da Mashawarcin Shugaban Kasa kan Harkokin Tsaro Mallam Nuhu Ribadu da wasu ministoci da Mashawarcin Shugaban Kasa na Musamman kan Harkokin Siyasa Ibrahim Kabir Masari da sauran manyan baki.

Shugaba Tinubu ya ce “Allah ya albarkaci Najeriya kuma ya mayar da bambance-bambancen da muke da su su zama sanadin samun wadata ga kasar.”

Shugaban ya yi wadannan kalamai ne bayan ya gudanar da aikin Umrah da sanyin safiyar Juma’a a Masallacin Harami da ke Makkah inda ya yi addu’ar samun zaman lafiya mai dorewa hadin kan kasa da kwanciyar hankali a Najeriya.

A yayin gudanar da ibada Shugaba Tinubu ya roki Allah ya ba shugabannin kasar shiriya ya karfafa zumuncin ‘yan’uwantaka a tsakanin ‘yan Najeriya tare da kawo karshen matsalolin tsaro da sauran kalubalen da kasar ke fuskanta.

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala ibadar Shugaban ya nuna godiyarsa ga Allah Madaukakin Sarki bisa damar da ya ba shi ta gudanar da Umrah inda ya jaddada muhimmancin zaman lafiya jituwa da imani ga makomar kasar.

Ya ce, “Mun yi addu’a ga kasarmu domin kowa ya rayu cikin zaman lafiya da jituwa farin ciki da imani ga Allah Madaukakin Sarki.” Shugaba Tinubu ya kuma bayyana kyakkyawan fata game da makomar tattalin arzikin Najeriya ci gaban al’umma da inganta tsaro. Ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na gina kasa mai zaman lafiya da hadin kai inda ‘yan kasa za su iya rayuwa cikin aminci da mutunci ba tare da la’akari da bambancin addini ko kabila ba.

Daga cikin manyan mutanen da suka halarci liyafar akwai Mashawarcin Shugaban Kasa kan Harkokin Tsaro Mallam Nuhu Ribadu Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani da Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya (Nigeria Governors’ Forum) wanda kuma shi ne Gwamnan Jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq.

Haka kuma wadanda suka halarci taron sun hada da Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a Lateef Fagbemi da Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a Farfesa Ali Pate. Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Femi Gbajabiamila da kuma Mai Ba Shugaban Kasa Shawara na Musamman kan Harkokin Siyasa Ibrahim Kabir Masari tare da wasu manyan jami’an gwamnati.

 

 

Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button