
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi tattaunawa da shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier a birnin Beijing inda ya bayyana shirin kasar Sin na karfafa dangantakar kasashen biyu da kuma bude wani sabon babi a cikin hadin gwiwarsu ta dabarun ci gaba.
Xi ya bayyana kasar Sin da Jamus kasashe na biyu da na uku mafi girma a duniya a matsayin kasashe masu manyan nauyi wajen inganta zaman lafiyar tattalin arzikin duniya da kuma karfafa dangantakar Sin da EU.
Ya bukaci kasashen biyu da su zurfafa sadarwa da hadin gwiwa su inganta daidaito da kuma cin gajiyar juna sannan su aika sako mai kyau ga duniya ta hanyar zabar “bude ido maimakon kadaici da hadin gwiwa maimakon rikici.”
Xi ya kuma karfafa wa Jamus gwiwa da ta rungumi ra’ayi mai kyau game da ci gaban kasar Sin yana mai jaddada cewa girmama juna da kuma daidaita juna suna da matukar muhimmanci don ci gaba da dorewar dangantakar kasashen biyu.
KARANTA KUMA: Alakar Kafafen Yada Labarai na Najeriya da China Za Su Iya Cike Gibin Al’adu da Ilimi
Dangane da hadin gwiwar tattalin arziki Xi ya nuna damammaki a fannin fasahar kere-kere makamashin kore tattalin arzikin dijital cinikayya a ayyuka da kuma masana’antu masu ci gaba.Ya yi maraba da ‘yan kasuwar Jamus da su fadada jarin su a kasar Sin yayin da ya bukaci Jamus da ta samar wa kamfanonin kasar Sin “yanayin kasuwanci mai adalci, gaskiya da kuma mara wariya.”
Ya kuma yi kira da a kara zurfafa musayar ra’ayoyi kan al’adu ilimi da fasaha kafin cika shekaru 55 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu a shekarar 2027.
Da yake jawabi game da dangantakar China da EU Xi ya jaddada cewa “hadin gwiwa ya fi karfin gasa kuma yarjejeniya ta fi karfin bambance-bambance.” Ya bukaci Turai da ta yi aiki tare da China don samar da duniya mai tsari da kuma ci gaban tattalin arzikin duniya mai hade da juna.
A martanin da ya mayar Steinmeier ya yaba da ci gaban tattalin arzik kimiyya da fasaha na kasar Sin yana mai sake jaddada kudirin Jamus na bin manufofinta na kasar Sin daya.
Ya bayyana kwarin gwiwa kan makomar dangantakar kasashen biyu yana mai cewa za a iya warware sabanin tattalin arziki da cinikayya ta hanyar tattaunawa da shawarwari don cimma “sakamakon cin nasara”.
Steinmeier ya kuma amince da karuwar matsin lamba kan tsarin kasa da kasa, sannan ya bayyana sha’awar Jamus na yin aiki tare da kasar Sin don kare zaman lafiya a duniya da kiyaye Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya da dokokin kasa da kasa da tallafawa cinikayya mai ‘yanci da kuma adawa da kariyar kai da yakin cinikayya.
Kafin taron an shirya wani biki na maraba da Xi da matarsa Peng Liyuan suka shirya wa Steinmeier da matarsa Elke Büdenbender. An kuma gudanar da wani liyafa na gwamnati a ranar Juma’a da yamma.
Taron ya nuna sabon kokarin da manyan tattalin arzikin duniya biyu ke yi na karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da diflomasiyya da kuma magance bambance-bambancen cinikayya da kuma bayar da gudummawa tare ga kwanciyar hankali a duniya a yayin da ake kara samun tashin hankali a duniya.
Xinhua/Aisha.Yahaya, Lagos



