Kasuwanci

Makarantar Caleb Ta Najeriya Ta Lashe Gasar Kirkire-Kirkire Ta Bankin Zenith

Makarantar Caleb British International School dake Abijo a jihar Legas ta lashe matsayi na daya a gasar kirkire-kirkire na Bankin Zenith (Zecathon 6.0) inda ta sami kyautar kudi har naira miliyan biyar.

Makarantar ta doke sauran wadanda suka kai matakin karshe daga sassan kasar nan ta hanyar gabatar da wani dandamali na zamani mai suna ‘ReLearn’. Wadanda suka jagoranci kirkirar wannan dandamali su ne Deborah Iweha Makayla Inyere Fife Alonge da kuma Okeke Janelle.

Wannan nasara ta nuna irin jajircewar makarantar wajen cimma kyakkyawan sakamako a fannin ilimi kirkire-kirkire a fannin fasaha da kuma koyo ta hanyar aikace-aikace.

KARANTA KUMA: Mataimakin Shugaban Kasa Shettima Ya Yabi Al’adar Kirkire-kirkire Ta Bankin Zenith A Cikin Shekaru 35

A cewar wanda ya kafa Jami’ar Caleb kuma Shugaban Rukunin Makarantun Caleb Dr. Oladega Adebogun wannan nasara tana nuna hangen nesa na ilimi na makarantar da kuma jajircewarta wajen bayar da ingantaccen ilimi wanda ke ci gaba da karfafa kirkire-kirkire tunani mai zurfi da kawo sababbin dabaru a tsakanin matasa.

Ya ce nasarar ta kara jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin cibiyoyin ilimi da bangaren masu zaman kansu wajen shirya matasa domin makomar da fasaha za ta taka rawar gani a cikinta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button