Jihar Akwa Ibom Ta Amince Da Biyan Karin Fansho Na Wata 13 Ga Masu Ritaya

Gwamnan Jihar Akwa Ibom Umo Eno ya amince da bayar da karin fansho na wata na 13 ga masu ritaya a jihar tare da tallafin jin dadin jama’a na lokaci guda na Naira 10,000 ga kowane mai karbar fansho a watan Nuwamba na shekarar 2026.
Gwamna Eno ya sanar da amincewar ne a yayin wani taro da kungiyar masu karbar fansho ta Najeriya NUP reshen jihar ta shirya inda aka ba shi lambar yabo ta cancanta tare da bayyana goyon bayan sake zabensa a shekarar 2027.
Gwamna Eno ya bayyana cewa wannan mataki na nuna godiya ne ga gudummawar da tsoffin ma’aikatan gwamnati suka bayar wajen ci gaban jihar.
Ya ba su tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da jajircewa wajen inganta jin dadin masu karbar fansho da tsofaffi.
Gwamnan ya yaba wa masu karbar fanshon bisa yadda suka tsara kansu da kuma nuna godiyarsu.
“Wannan abu ne da ya taba zuciyata matuka. Yana nuna cewa ku kwararru ne na gaske masu tsari mai ban sha’awa. Ko da yake kun yi ritaya amma ba ku gajiya ba. Ina girmama ku kuma ina matukar godiya a gare ku.
Yanzu haka na bayar da umarnin a kara Naira 10,000 a kan kudin fanshon watan Nuwamba na 2026 ga kowane mai karbar fansho domin tallafawa jin dadinku” in ji shi.
Tsarin Inshorar Lafiya
Ya yi kira ga masu karbar fansho masu shekaru 65 zuwa sama da su yi rajista a tsarin inshorar lafiya na jihar wanda ya ce yana ba da kulawar lafiya kyauta ga wannan rukuni na shekaru domin sauƙaƙa musu samun damar kula da lafiyarsu.
Game da kudaden sallama da ba a biya ba Eno ya bayyana cewa gwamnatinsa ta biya Naira biliyan 100 daga cikin bashin Naira biliyan 111 da ta tarar wanda ya tara tun daga shekarar 2012.
Ya ba da tabbacin cewa za a biya sauran kudaden da ake bin gwamnati kafin kammala wa’adinsa na farko inda ya danganta wannan ci gaba da karuwar kudaden shiga da gwamnatocin jihohi ke samu a karkashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Sake Zabe
Saboda haka Gwamnan ya yi kira ga masu karbar fansho da su goyi bayan sake zaben Shugaba Tinubu a shekarar 2027 yana mai cewa ci gaba da mulkinsa zai tabbatar da samun kudade don ci gaba da biyan kudaden fansho kudaden sallama da sauran alawus-alawus na jin dadin rayuwa.
Ya kuma yi kira ga masu karbar fansho musamman wadanda suka fito daga Gundumar Sanata ta Ikot Ekpene da su goyi bayan sake zaben Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio.
Shugaban Kungiyar Masu Karbar Fansho ta Najeriya NUP na kasa Mazi Godwin Abumisi ya yaba wa Gwamna Eno saboda nuna kulawa ta musamman da kuma damuwa game da jin dadin tsoffin ma’aikata a jihar Akwa Ibom.
Abumisi ya yaba da salon shugabancin Gwamnan da kuma shirye-shiryensa na ci gaba tare da yin kira ga masu karbar fansho a fadin jihar da su goyi bayan sake zabensa a shekarar 2027.
A cikin jawabinsa na maraba Shugaban kungiyar na jihar Sylvester Nkodo ya bayyana kokarin Gwamnan na inganta rayuwar tsofaffi da tsoffin ma’aikatan gwamnati a matsayin abin farin ciki da kuma wani abu da ba a taba ganin irinsa ba a baya.
Nkodo ya ce Gwamna Eno ya nuna jajircewa wajen magance matsalolin masu karbar fansho ta hanyar aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da suka inganta yanayin rayuwarsu tare da dawo da mutuncinsu a matsayinsu na tsoffin ma’aikata.
Ya kuma nuna godiya kan fitar da sama da Naira biliyan 100 domin biyan tsoffin basussukan kudaden sallama da aka tara tun daga shekarar 2012 tare da yin kira ga mutane su yi addu’a da kuma ba da goyon baya ga burin Gwamnan na yin wa’adi na biyu.
Daga baya masu karbar fansho sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Tinubu Shugaban Majalisar Dattawa Akpabio Gwamna Eno da sauran ‘yan takarar jam’iyyar APC domin sake zaben su a shekarar 2027.
Wannan goyon baya ya biyo bayan wani kuduri da Comrade James Inim ya gabatar wanda kuma Dr. Uduak Udoaka ya goyi baya inda dukkan mahalarta taron suka amince da shi baki daya.
Taron ya samu halartar tsoffin ma’aikata masu karbar fansho da dama wadanda wasu daga cikinsu suka ci gaba da zama a wurin taron duk da ruwan sama domin halartar bikin da kuma nuna godiyarsu ga Gwamnan.



