Najeriya

Fani-Kayode Ya Fara Gudanar Da Aiki A Matsayin Jakadan Najeriya A Afirka Ta Kudu

Babban Kwamishinan Najeriya a Afirka ta Kudu Jakada Femi Fani-Kayode ya fara gudanar da ayyukansa na diflomasiyya a hukumance bayan ya mika kwafin takardun shaidar nadinsa ga Ma’aikatar Harkokin Kasashen Waje da Hadin Gwiwa ta kasar (DIRCO).

Fani-Kayode ya mika takardun a ranar Juma’a 30 ga watan Oktoba ga Mista Clayson Monyela Mataimakin Darakta-Janar mai kula da Harkokin Diflomasiyya da Jama’a wanda kuma ke rike da mukamin Shugaban Sashen Kula da Ka’idojin Gwamnati (Chief of State Protocol) a ma’aikatar ta DIRCO.

Wata sanarwa daga Kakakin Ma’aikatar Harkokin Kasashen Waje ta Najeriya Oluwafemi Adeniyi ta bayyana cewa mika wadannan takardu ya zama alamar fara gudanar da ayyukan diflomasiyya na Babban Kwamishinan a hukumance tare da ba shi ikon wakiltar Najeriya a Afirka ta Kudu a madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

KARANTA KUMA: Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama Fani Kayode Ya Shiga APC

Wannan ci gaban ya biyo bayan wani sauyi da aka samu kwanan nan a yarjejeniyar diflomasiyya ta Afirka ta Kudu wanda a karkashinsa ake ganin wani shugaban tawagar ya fara aiki bayan ya mika kwafin Wasikun Nadin Mukaminsa ga Yarjejeniyar Shugaban Kasa. Daga baya an gabatar da takardun farko ga Shugaban kasar a wani bikin bayar da takardar shaidar aiki.

Bayan gabatar da takardar Fani-Kayode ya yi taron gabatarwa da Ambasada Seboga Mataimakin Darakta Janar na DIRCO a matsayin wani bangare na tattaunawar diflomasiyya da ya yi da manyan jami’an gwamnatin Afirka ta Kudu.

A lokacin taron Babban Kwamishina na Najeriya ya bayyana kwarin gwiwarsa kan yiwuwar karfafa dangantakar kasashen biyu tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu.

Ya jaddada bukatar sabunta hadin gwiwa da kuma kawancen dabaru musamman a fannoni masu amfani ga kasashen biyu.

Gabatarwar ta nuna farkon huldar diflomasiyya ta Fani-Kayode a Afirka ta Kudu inda shi ma aka amince da shi a Masarautun Lesotho da Eswatini a lokaci guda.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button