Shugaba Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Kamene Okonjo mahaifiyar shugabar WTO

Shugaba Bola Tinubu ya mika sakon ta’aziyya ga gidan sarautar Okonjo na Ogwashi-Uku a Jihar Delta biyo bayan rasuwar Farfesa Kamene Okonjo wacce ta rasu tana da shekaru 96 a duniya.
A cikin wani sakon ta’aziyya da mai magana da yawunsa Bayo Onanuga ya sanya wa hannu Shugaban ya nuna alhininsa ga ‘yarta Dr. Ngozi Okonjo-Iweala wacce ita ce Darakta-Janar na Hukumar Ciniki ta Duniya (WTO) da sauran ‘yan uwa da kuma al’ummar Ogwashi-Uku.
KARANTA KUMA: Shugaba Tinubu Ya Yi Makokin Jakada Dele Cole Ya Yaba Gudunmawarsa a Fannin Aikin Jarida
Shugaba Tinubu ya bayyana marigayiya Farfesa Okonjo a matsayin kwararriyar masaniya a fannin ilimi wacce rayuwarta ta kasance mai cike da hazaka ta fannin tunani hidima ga bil’adama da kuma jajircewa wajen karfafa mata da ci gaban al’umma.
Ya kuma yaba da gudunmawar da ta bayar a fannin ilimi da kuma sadaukarwarta ga iyalinta al’ummarta da kuma kare tsarin gargajiya.
Shugaban ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya ba wa Farfesa Okonjo hutu na har abada, Ya kuma ba da hakuri da juriya ga iyalinta da dukkan wadanda ke jimamin rasuwarta.
Aisha.Yahaya, Lagos



