Zanga-Zangar Nuna Adawa Da Yaƙi Da Tashin Farashin Kaya Ta Barke A Manyan Biranen Italiya

Zanga-zangar adawa da yaki da hauhawar farashin rayuwa ta mamaye manyan biranen Italiya a ranar Asabar inda aka ruwaito barkewar rikici a Turin Rome da Bologna mako guda bayan barkewar rikici a fadin kasar.
Hukumomin sun tura jami’an ‘yan sanda da yawa kuma shaguna da yawa sun rufe a matsayin rigakafin barna da ka iya faruwa.
Zanga-zangar ta biyo bayan rikicin da ya faru a karshen makon da ya gabata inda masu zanga-zanga suka yi fada da ‘yan sanda suka wawushe shaguna suka lalata kadarori. Zanga-zangar ta ranar Asabar ta kasance cikin lumana a Milan yayin da aka yi arangama tsakanin masu zanga-zanga da ‘yan sanda a Turin Rome da Bologna.
KARANTA KUMA: Italiya Ta Amince Da Sabbin Dokokin Zabe Kafin Zaben 2027
Shaidu ‘yan jarida ba su ga an wawushe shaguna ko an lalata kadarori a zanga-zangar ranar Asabar ba.
Hukumomin sun kara tsaurara matakan tsaro bayan da aka yi kira da a ci gaba da zanga-zangar a shafukan sada zumunta a cikin makon suna neman hana sake afkuwar tashin hankalin da ya faru a karshen makon da ya gabata.
A safiyar ranar Asabar ‘yan sandan Italiya sun ce sun kama wani mutum da ake zargin yana da alaka da shirya “Movement na 17 ga Oktoba” wanda aka danganta da zanga-zangar karshen makon da ya gabata. An kai mutumin hedikwatar ‘yan sanda a Milan don yi masa tambayoyi.



