Kwararrun ECOWAS Sun Gudanar Da Taro Don Inganta Samar Da Mujallar Al’adu

Hukumar Ƙungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta hannun Daraktan Ilimi Kimiyya da Al’adu na Hukumar ta shirya wani taron fasaha na yanki a birnin Lomé na ƙasar Togo wanda ke da nufin tabbatar da kalandar al’adu ta ECOWAS tare da samar da mujallar al’adu ta ƙungiyar.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a shafin yanar gizo na Hukumar ECOWAS an bayyana cewa taron ya tattaro kwararru a fannin al’adu daga ƙasashen da ke mamba a ƙungiyar ta ECOWAS.

Wannan taro wani bangare ne na kokarin da Hukumar ECOWAS ke yi “don inganta masana’antun al’adu da na kirkire-kirkire da kasuwar kayayyaki da ayyukan al’adu a yankin da karfafa tsarin gudanarwa da tsarin bayanan al’adu a yankin tare da bayyana bambance-bambancen bayyanar al’adu da bukukuwa daban-daban a Yammacin Afirka.”
KARANTA KUMA: ECOWAS Na Matakan Karfafa Ayyukan Taimako A Lokacin Bala’i A Fadin Yammacin Afirka
Da yake jawabi a taron Daraktan Ilimi Kimiyya da Al’adu na Hukumar ECOWAS Dr. Roland Kouakou wanda Kwamishinan Ci Gaban Dan Adam da Harkokin Jama’a Farfesa Nassirou Bako-Arifari ya wakilta ya bayyana cewa “ECOWAS na da burin karfafa tsarin bayanan al’adu da hadin gwiwa tsakanin kasashe mambobi, tare da tallafawa bunkasa da kuma bayyana masana’antun al’adu da na kirkire-kirkire a fadin Yammacin Afirka.”
Hukumar ECOWAS tana kuma aiwatar da shirye-shirye na dabarun da ke da nufin zurfafa hadin kan yankin da kuma kawar da cikas ga hadewar kasashen.
Wadannan matakai sun yi daidai da ‘Hangen Nesa na ECOWAS na 2050’ (ECOWAS Vision 2050) wanda ke da nufin sauya kungiyar daga kasancewa “ECOWAS ta Jihohi” zuwa “ECOWAS ta Jama’a” tare da inganta zaman lafiya wadata da kuma ba da damar shigar ‘yan kasa sosai a harkokin yankin.



