Shugaba Tinubu Ya Isa Kaduna Domin Kaddamar Da Yakin Neman Zaben Jam’iyyar APC

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya isa Jihar Kaduna domin kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a hukumance gabanin babban zaben shekarar 2027.
Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima da Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani ne suka tarbi Shugaban.

Gwamnoni Ministoci Sanatoci sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar APC jami’an da aka zaba da kuma magoya baya daga sassa daban-daban na kasar nan sun taru a filin wasa na Kaduna Township Stadium domin gudanar da taron gangami wanda ke nuna kaddamar da yakin neman zaben jam’iyyar a hukumance domin sake zaben Tinubu.
KARANTA KUMA: Magoya Baya Sun Cika Filin Wasa Na Kaduna Domin Taron Kaddamar Da Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Na Jam’iyyar APC


Ana sa ran taron zai kunshi gabatar da tsarin jam’iyyar na ‘Renewed Hope 2.0’ (Sabon Bege 2.0) wanda ke bayyana muhimman abubuwan da ta sa a gaba yayin da jam’iyyar APC ke fara ayyukan yakin neman zabenta gabanin zaben shekarar 2027.


Taron yana kuma zama dandamali ga jam’iyyar domin tattara magoya bayanta da kuma bayyana abin da ta dauka a matsayin nasarorin gwamnatin Tinubu yayin da take neman wa’adi na biyu a kan karagar mulki.



