Siyasa

Kaddamar Da Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Na Jam’iyyar APC Ya Hada Manyan Mutane

Manyan jiga-jigan mutane sun fara isa filin wasa na Kaduna Township inda za a gudanar da taron kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar  APC domin sake zaben Shugaba Bola Tinubu a shekarar 2027.

Daga cikin wadanda suka fara isa akwai Sakataren Gwamnatin Tarayya Sanata George Akume tare da wasu Ministoci Sanatoci da kuma ‘yan Majalisar Wakilai.

Ana sa ran karin shugabannin siyasa da manyan baki za su iso wurin kafin fara taron.

KARANTA KUMA: Tsammani Ya Yi Yawa Yayin Da APC Ke Kaddamar Da Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa

Filin wasan ya riga ya cika da yanayi na zumudi yayin da magoya bayan jam’iyya da kungiyoyin siyasa ke jiran isowar Shugaba Tinubu wanda ake sa ran zuwansa zai zama alamar kaddamar da ayyukan yakin neman zabe a hukumance.

Ana sa ran taron zai samu halartar shugabannin jam’iyyar APC jami’an da aka zaba, da kuma magoya baya daga sassan kasar nan, yayin da jam’iyyar ke fara shirye-shiryen tara jama’a a fadin kasar domin zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

A daya bangaren kuma, tutocin da ke dauke da hotunan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaba Kashim Shettima sun kara armashi ga taron kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a filin wasa na Kaduna Township Stadium.

Tutocin wadanda magoya baya daga kungiyoyin siyasa daban-daban suka daga sun bambanta ta fuskar launuka zane-zane da girma. Hakan ya haifar da yanayi mai cike da armashi da kuzari yayin da magoya bayan jam’iyyar suka taru don nuna goyon bayansu ga sake zaben Shugaba Tinubu da kuma takarar Mataimakin Shugaban Kasa Shettima gabanin zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button