Kaduna Ta Shirya Tsaf Domin Taron Yakin Neman Zaben Shugaba Tinubu

Jihar Kaduna na shirin karbar bakuncin Shugaba Bola Tinubu a ranar Asabar domin kaddamar da gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Ana sa ran taron zai samu halartar shugabannin jam’iyya da jami’an da aka zaba da kuma magoya baya daga sassan Najeriya daban-daban.
A filin wasa na Kaduna Township Stadium inda za a gudanar da taron shirye-shirye sun kusan kammalawa yayin da masu shirya taron ke sanya hannun karshe kan kayayyakin da za a yi amfani da su a wannan muhimmin taron siyasa.
An kawata wurin zama na musamman (VIP) tare da sanya na’urorin sanyaya iska sannan an tanadi wasu tantuna da kuma shirya kujeru domin daukar mahalarta taron.
KARANTA KUMA: Uwargidan Shugaban Kasa Za Ta Jagoranci Gangamin Jam’iyyar APC a Yankin Arewa ta Tsakiya
An kuma kara tsaurara matakan tsaro a fadin birnin Kaduna inda aka tura jami’an ‘Yan Sandan Najeriya Sojojin Najeriya da kuma Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya zuwa muhimman wurare domin tabbatar da tsari da kuma kare lafiyar wadanda za su halarci taron.
An sanya fastoci da allunan talla dauke da hotunan Shugaba Tinubu da Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani a wurare daban-daban a cikin birnin wanda hakan ke nuna yadda shirye-shiryen taron ke kara karfi.
Ana sa ran cewa taron kaddamar da yakin neman zaben wanda aka tsara gudanarwa a ranar Asabar 24 ga watan Oktoba 2026 zai hada gwamnonin jam’iyyar APC ‘yan majalisar dokoki ta kasa da na jihohi, shugabannin kananan hukumomi da kansiloli, tare da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar daga sassa daban-daban na kasar.
Ana kallon taron a matsayin wata babbar dama ga jam’iyyar mai mulki wajen tara ma goyon baya ga sake zaben Shugaba Tinubu a shekarar 2027 tare da karfafa tsarin siyasar jam’iyyar gabanin babban zaben.
Wannan taro ya zo ne a daidai lokacin da jam’iyyun siyasa a fadin kasar ke ci gaba da shirye-shiryen karfafa tushen magoya bayansu, tuntubar masu zabe, da kuma gabatar da tsare-tsarensu gabanin zaben shekarar 2027.
Aisha.Yahaya, Lagos



