Kasuwanci

CBN Ta Kai Tallar Damar Kuɗaɗen Najeriya Zuwa Birnin Beijing

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kira wani babban taron tattaunawa kan harkokin kasuwanci da harkokin kudi a birnin Beijing na kasar Sin domin binciko hanyoyin zurfafa kasuwannin kudi na Najeriya da kuma karfafa hanyoyin hada-hadar kudi tsakanin kasashen biyu.

Taron, wanda aka gudanar a karkashin taken, “Ƙarfafa Tsarin Kudi na Najeriya da China” ya bai wa ‘yan kasuwa da ke aiki a kasuwannin biyu damar tattaunawa kan dangantakar banki haɗin gwiwa da hanyoyin saka hannun jari.

Gwamnan CBN Olayemi Cardoso ya jaddada muhimmancin yin mu’amala kai tsaye da ‘yan kasuwa don fahimtar damammaki da kalubalen da ke tsara ayyukan kudi tsakanin Najeriya da China.

KARANTA KUMA:http://China da Koriya ta Arewa sun bude gadar iyaka don bunkasa ciniki

Cardoso ya ce hadin gwiwar zai taimaka wa Bankin wajen samar da dabarun gina kasuwannin kudi masu zurfi da kuma saukin shiga.

Mataimakin Gwamnan CBN kan Manufofin Tattalin Arziki Philip Ikeazor ya jaddada bukatar sauya ingantattun muhimman hanyoyin tattalin arziki zuwa karuwar saka hannun jari da kuma kasuwannin kudi masu ci gaba.

An kuma yi wa mahalarta bayani kan ci gaban gyaran tattalin arzikin Najeriya ingantattun muhimman hanyoyin tattalin arziki da kuma damar saka hannun jari da ke tasowa a kasuwannin kudi na kasar.

Taron na Beijing ya kasance wani ɓangare na babban dabarun CBN na ƙarfafa dangantakar kuɗi ta Najeriya a faɗin Asiya.

Ya biyo bayan irin wannan hulɗa a Singapore da kuma yayin taron shekara-shekara na Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya a Bangkok.

Shirin Bankin a China ya kuma haɗa da tattaunawa tsakanin ɓangarorin biyu da Bankin Jama’a na China hulɗa da shugabannin Bankin Masana’antu da Kasuwanci na China (ICBC) da kuma tarurruka da ‘yan kasuwan Najeriya da China.

An yi wannan hulɗar ne don fahimtar ƙalubalen kuɗi da ‘yan kasuwa ke fuskanta da kuma binciko hanyoyin ƙarfafa hanyoyin aika kuɗi da kuma sauƙaƙe saka hannun jari a Najeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button