Ƙungiyar Aiki Na Shugaban Ƙasa Sun Gabatar Da Kudirin Dokar ‘Yan Sanda Na Ƙasa Domin Dubawa

Kwamitin Aiki na Shugaban Kasa kan Kudirin Dokar ‘Yan Sanda na Kasa ya kammala matakin tsara daftarin aikin da aka dora masa kuma ya mika daftarin Kudirin Dokar ‘Yan Sanda na Kasa na shekarar 2026—tare da wasu kudirori 29 na gyare-gyaren dokoki masu alaka da shi—ga Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya domin a duba su ta fuskar tsarin doka tare da tantance ingancinsu.
Shugaban Kwamitin wanda kuma shi ne Babban Jami’in Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Femi Gbajabiamila ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa an mika wadannan daftarin dokoki ga Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a a ranar Litinin 19 ga watan Oktoba 2026 daidai da tsarin aikin da aka amince wa Kwamitin su bi.
Gbajabiamila ya bayyana cewa Ma’aikatar Shari’ar za ta gudanar da cikakken bincike na doka kan daftarin dokokin domin tabbatar da cewa sun yi daidai da ka’idoji da tsare-tsaren da aka amince da su wajen tsara dokoki tare da duba ko akwai wani karo da dokokin da ke aiki a halin yanzu.
Ya kara da cewa ana sa ran Ma’aikatar Shari’ar za ta kammala aikin tantancewar sannan ta mayar da daftarin dokokin ga Kwamitin a ranar Juma’a 30 ga watan Oktoba 2026 ko kafin wannan ranar.
A cewarsa bayan haka Kwamitin zai sake duba daftarin dokokin a karo na karshe kafin ya gabatar da su ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu matakin da zai zama kammala aikin da aka ba wa Kwamitin a hukumance.

Kudirin dokar ‘yan sanda na kasa da aka gabatar yana da nufin kafa tsarin doka da na kundin tsarin mulki domin samar da tsarin ‘yan sanda mai bangarori biyu a Najeriya wato rundunar ‘yan sandan tarayya da kuma rundunonin ‘yan sandan jihohi.
Sanarwar ta kara bayyana cewa shirya wannan kudirin dokar ‘yan sanda na kasa yana tafiya ne tare da aikin duba kudirin gyaran Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 (Gyara na Shida) da majalisun dokokin jihohi ke gudanarwa a halin yanzu tsari ne da dole ne a kammala shi kafin a mika kudirin dokar ‘yan sandan ga Majalisar Dokokin Tarayya.
Gbajabiamila ya sake jaddada kudurin tawagar aikin na ganin an bi tsari mai zurfi da gaskiya domin samar da cikakken tsarin doka wanda za a gabatar wa Shugaban Kasa sannan daga baya a mika shi ga Majalisar Dokokin Tarayya.
Aisha.Yahaya, Lagos



