2027: Darakta Janar Na Kamfen Din APC Ya Yi Alkawarin Gudanar Da Shawarwari Da Suka Shafi Kowa

Darakta-Janar na Majalisar Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Sanata Abdulaziz Yari ya bai wa masu ruwa da tsaki tabbacin cewa za a sanya su a cikin harkokin da suka shafi shirye-shiryen babban zaben shekarar 2027.
Yari wanda ke wakiltar Mazabar Sanata ta Zamfara ta Yamma ya bayar da wannan tabbacin ne yayin ziyarar tuntuba ga Sarakunan Gwandu Katsina Daura da Zariya a matsayin wani bangare na kokarin shigar da masarautun gargajiya cikin shirye-shiryen zaben.
Wata sanarwa daga ofishin yada labaransa ta bayyana cewa ziyarorin na daga cikin rangadin tuntuba a fadin kasar wanda ke da nufin samar da fahimtar juna da kuma tara goyon baya gabanin gudanar da muhimman ayyukan yakin neman zabe.
Wadannan ziyarori sun biyo bayan wasu tarurruka makamantan haka da aka gudanar tare da Ooni na Ife Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi da kuma Sarkin Ilorin Alhaji Ibrahim Kolapo Sulu-Gambari.
KARANTA KUMA: Majalisar Yakin Neman Zaben APC Ta Yi Alkawarin Mayar da Hankali Kan Batutuwan da suka Shafi Cigaba
A yayin tarurrukan sarakunan gargajiyar sun yi addu’o’i tare da bayar da albarka domin samun zaman lafiya hadin kai da kuma nasarar tsarin dimokuradiyyar Najeriya.

Yari ya ce hulɗa da cibiyoyin gargajiya muhimmin ɓangare ne na dabarun tattaunawa na majalisar yana mai jaddada cewa ba an yi niyyar ziyarar ne don neman amincewar siyasa ba sai dai don neman addu’o’i albarka da shawarwari daga sarakuna.
Jagorar Dabi’a
Ya lura cewa sarakunan gargajiya sun kasance masu mahimmanci wajen haɓaka zaman lafiy haɗin kai da kwanciyar hankali yana mai cewa jagorancin ɗabi’arsu yana da mahimmanci ga tsarin siyasa na ƙasar.
Majalisar Yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa ta APC ta nanata girmama cibiyoyin gargajiya da gudummawar da suke bayarwa ga ci gaban ƙasa tana mai ba da tabbacin cewa za a ci gaba da dukkan masu ruwa da tsaki a shirye-shiryen babban zaɓen 2027.

Wadanda suka raka Yari a ziyarar sun hada da tsohon gwamnan jihar Borno Sanata Ali Modu Sherif tsohon gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje tsohon gwamnan jihar Kebbi Sanata Adamu Aliero da tsohon gwamnan jihar Zamfara Sanata Sani Ahmad Yarima.
Sauran sun hada da tsohon gwamnan jihar Sokoto Sanata Aliyu Wamakko tsohon gwamnan jihar Gombe Sanata Muhammad Danjuma Goje da tsohon gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shehu da dai sauransu.
Aisha.Yahaya, Lagos



