Zelenskiy Na Fatan Ganin An Yi Ganawar Amurka Da Rasha A Yayin Taron Kolin G20

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskiy ya bayyana fatansa na ganawa da wakilan Amurka da Rasha a yayin taron kolin kungiyar kasashe 20 masu karfin tattalin arziki (G20).
A cikin wata tattaunawa da manema labarai ta manhajar WhatsApp Zelenskiy ya ce “Ana iya gudanar da taron a Amurka yayin taron kolin na G20. Sai dai har yanzu babu wani tabbaci daga bangaren Rasha ko na Amurka. Haka kuma ana iya gudanar da shi a wata kasa ta Turai.”
Ya kara da cewa “Ana iya gudanar da taron a daya daga cikin kasashen Gabas ta Tsakiya. Amurka ta sha ambaton kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa ko Saudiyya a matsayin wuraren da za a iya yin hakan.”
KARANTA KUMA: Tattaunawar Amurka Da Rasha Kan Ukraine Ta Fadada Zuwa Yarjejeniyar Man Fetur Ta Biliyoyin Daloli
Zelenskiy ya bayyana cewa wakilan Ukraine sun tattauna da jami’an Amurka a ranar Juma’a amma bai bayar da karin bayani ba. Ya kuma ce ya kamata Turai ta samar da nata tsarin tattaunawa da Rasha.
Kungiyar kasashe 20 masu karfin tattalin arziki (G20) wadda ta kunshi Amurka da Rasha amma ba ta hada da Ukraine ba ta shirya gudanar da taron kolinta a birnin Miami a watan Disamba.



