Sand Eagles Sun Sha Kashi A Hannun Ghana Ta Hanyar Bugun Fenariti A Wasan Neman Cancantar Shiga Gasar BSAFCON.

Kungiyar kwallon kafa ta bakin teku ta Najeriya Sand Eagles ta sha kashi a hannun Ghana ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron gida (4-5) bayan sun tashi kunnen doki 4-4 a lokacin karin lokaci a wasan farko na neman cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka na kwallon kafa ta bakin teku (BSAFCON) na shekarar 2026 wanda aka gudanar a Kaduna ranar Asabar da ta gabata.
Isa Hamza Manga ya nuna bajinta sosai ga Najeriya inda ya zura kwallaye uku (hat-trick) ciki har da kwallon farko yayin da Super Sand Eagles suka yi gwagwarmayar ci gaba da fafatawa da kungiyar Black Sharks.
Ekene Obi shi ma ya zura kwallo a lokacin karin lokaci amma Najeriya ba ta samu nasara ba yayin da Ghana ta yi kokarin ramawa har aka kai ga bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Mawuli Sosu ya zura kwallaye biyu ga Black Sharks yayin da Wise Nyamadi ya zura kwallon da ta daidaita sakamakon wasan a lokacin karin lokaci lamarin da ya sa aka tashi kunnen doki bayan kammala lokacin wasa na yau da kullum da kuma karin lokaci.
Sand Eagles Sun Sake Shan Kashi da Ci 4-6 a Hannun Senegal
Daga karshe Ghana ta samu nasara da ci 5-4 a bugun daga kai sai mai tsaron gida lamarin da ya bai wa Black Sharks damar samun gaba kafin wasan na biyu da aka tsara za a yi a Keta a ranar Lahadi mai zuwa.
Yanzu dole ne Sand Eagles su nuna bajinta sosai a wasan da za su buga a wajen gida domin ci gaba da fatan samun tikitin shiga gasar ta nahiyar Afirka. Wanda ya yi nasara a jimillar wasannin biyu zai samu gurbi a gasar BSAFCON ta shekarar 2026 da za a gudanar a Senegal.
NFF/Aisha.Yahaya, Lagos



