Duniya

Harbin Jama’a A Pennsylvania Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane Tara.

An tabbatar da mutuwar mutane tara bayan wani harin bindiga a birnin Erie jihar Pennsylvania ta Amurka kamar yadda Gwamna Josh Shapiro ya bayyana.

Harin ya faru ne a daren Juma’a inda masu bincike suka gano cewa dukkan mutanen tara sun riga sun mutu kafin ‘yan sanda su isa wurin a cewar wata sanarwa da birnin Erie ya fitar.

Shapiro ya ce ya tattauna da Magajin Garin Erie Daria Devlin tare da ba da tabbacin cikakken goyon bayan gwamnatin jihar bayan faruwar lamarin.

“Na tattauna da Magajin Gari Devlin kuma na ba da tabbacin cikakken goyon bayan gwamnatina bayan wannan mummunan harin bindiga a Erie a daren jiya wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane tara daga cikin ‘yan uwarmu mazauna Pennsylvania” cewar Shapiro a wani sako da ya wallafa a shafin X.

KARANTA KUMA: Austria Ta Gabatar Da Dokokin Bindiga Masu Tsauri Bayan Harin Bindiga A Makaranta

Kwamishinan ‘Yan Sandan Erie Rick Lorah ya bayyana wurin da lamarin ya faru a matsayin daya daga cikin wurare mafi wahalar da ya taba cin karo da su a tsawon lokacin da yake aiki.

“Asarar rayuka abu ne mai matukar bakin ciki kuma yanayin da muke ciki yana da matukar tayar da hankali” in ji Lorah.

Ya kara da cewa masu bincike na ci gaba da aiki domin gano dalilin da ya sa aka kai harin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button