Shugaba Tinubu Ya Ba Da Tabbacin Daukar Matakin Ceto Yaran Da Aka Sace A Borno.

Shugaba Bola Tinubu ya bai wa Gwamnan Jihar Borno Babagana Zulum tabbacin cewa hukumomin tsaron ƙasa za su ɗauki matakan da suka dace domin ceto yaran da aka sace daga yankunan Lassa da Mussa a ƙaramar hukumar Askira/Uba da sauran sassan jihar Borno.
Farfesa Zulum ya bayyana hakan ne ga manema labarai na fadar shugaban ƙasa bayan ganawa da Shugaba Tinubu a fadar da ke Abuja inda ya bayyana damuwarsa game da hare-haren da aka kai wa al’ummomi kwanan nan da kuma ci gaba da riƙe yaran da aka sace a hannun masu garkuwa da mutane.
Gwamnan ya ce tabbacin da Shugaban ƙasar ya bayar ya biyo bayan bayanan da ya gabatar game da ƙalubalen tsaro da ke fuskantar Lassa Mussa da sauran yankuna masu rauni a ƙaramar hukumar Askira/Uba da kuma faɗin jihar baki ɗaya.
KARANTA KUMA: Sace-Sacen Mutane A Kebbi: Minista Ya Bai Wa Yara ‘Yan Najeriya Tabbacin Tsaro
“Shugaban ƙasa ya ba ni tabbacin cewa Sojojin Najeriya da ofishin Darakta-Janar na hukumar DSS da kuma ofishin Mai ba da Shawara kan Harkokin Tsaro na Ƙasa za su ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da cewa an ceto waɗannan yara da aka sace” cewar Gwamnan.
Da yake magana kan yanayin tsaro gaba ɗaya a jihar Borno Gwamnan Zulum ya ce jihar ta samu gagarumar ci gaba a cikin watanni shida da suka gabata tare da ci gaba da ƙoƙarin dawo da tsaro da ƙarfafa shi a wuraren da suke cikin haɗari. A cewarsa gwamnatin jihar ta taimaka wajen mayar da sama da mutane miliyan biyu da suka rasa muhallansu zuwa garuruwansu na asali a cikin shekaru bakwai da suka gabata yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin sake farfado da sauran wuraren zama.
Ya bayyana Kareto wani muhimmin yanki da ke tsakanin Damasak da Gubio a matsayin daya daga cikin wuraren da ke bukatar kulawa ta gaggawa sakamakon barazanar tsaro da ke ci gaba da faruwa a wannan hanyar mai tsawon kusan kilomita 100.
Gwamna Zulum ya nuna kwarin gwiwar cewa kafa rundunar soji a Kareto zai karfafa ayyukan tsaro sosai tare da magance hare-haren da ake ta kaiwa a kan hanyar.
Har ila yau ya bayyana shirye-shiryen sake bude hanyar Maiduguri–Damboa–Biu wadda ta kasance babban abin damuwa ga mazauna yankin da suka tilasta yin tafiya ta jihar Gombe domin isa Biu da sauran yankunan da ke makwabtaka da ita.
Gwamnan ya bayyana cewa madadin hanyar da ake bi a yanzu tana bukatar tafiyar kilomita 600 zuwa 700 idan aka kwatanta da tafiyar kilomita 200 kacal ta hanyar kai-tsaye lamarin da ke kara kudin sufuri da kuma tsawon lokacin tafiya.
Ya bayyana cewa Babban Hafsan Sojin Kasa ya dauki matakan horar da jami’an tsaron dazuzzuka (forest guards) kimanin 1,000 wadanda ake sa ran tura su aiki tsakanin watannin Nuwamba da Disamba domin karfafa ayyukan tsaro da kuma ba da damar sake bude wannan muhimmiyar hanya.
Haka kuma Gwamna Zulum ya bayyana shirye-shiryen sake kafa garin Sabon Gari a matsayin wani bangare na matakan karfafa nasarorin da aka samu a fannin tsaro da kuma farfado da harkokin tattalin arziki da zamantakewa a yankunan da rikici ya shafa a baya.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa sabbin matakan tsaro za su shafi al’ummomin da ke cikin mawuyacin hali a kananan hukumomin Chibok da Askira/Uba musamman wuraren da hare-haren suka shafa kwanan nan.
Dangane da binciken mai a Arewa maso Gabas Gwamna Zulum ya sanar da cewa Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya sanar da shirin ci gaba da ayyukan bincike a Jihar Borno da sauran sassan yankin.
Ya bayyana cewa an dakatar da ayyukan bincike na tsawon kimanin shekara daya zuwa biyu saboda kalubalen dabaru amma ya bayyana cewa Hukumar Binciken Frontier ta sanar da gwamnatocin jihohin da abin ya shafa a hukumance game da niyyarsu ta ci gaba da aiki.
“Mun sami bayanai daga Sashen Binciken Frontier na NNPCL cewa nan ba da jimawa ba za su zo su ci gaba da binciken mai a jihohin arewa maso gabas musamman Jihar Borno” in ji shi.
Gwamna Zulum ya tabbatar da cewa ya sami wasiku na hukuma kan shirin sake fara binciken yana mai nuna kwarin gwiwa cewa ayyukan bincike za su sake farawa a jihar nan ba da jimawa ba.



