Gwamnan Akwa Ibom Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Wadanda Suka Mutu A Hatsarin Jirgin Sama

Gwamnan Jihar Akwa Ibom Umo Eno ya mika sakon ta’aziyya ga Babban Hafsan Rundunar Sojin Sama (Chief of the Air Staff) Air Marshal Sunday Aneke da kuma iyalan mutane 25 da suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin saman Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) kirar ATR-42 a Jihar Ondo.
Gwamnan ya bayyana matukar bakin cikinsa game da wannan hatsari mai ban tausayi wanda kuma ya yi sanadiyyar mutuwar wani dan asalin Jihar Akwa Ibom marigayi Ukeme David.
A cikin sakon ta’aziyyar Gwamna Eno ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi tare da nuna alhininsa ga iyalan jaruman jami’an soji da fararen hula da suka rasa rayukansu a hatsarin.
“A madadin Gwamnati da al’ummar Jihar Akwa Ibom ina mika sakon ta’aziyya ta musamman ga Babban Hafsan Rundunar Sojin Sama Air Marshal Sunday Kelvin Aneke da iyalan danmu Ukeme David wanda yana daya daga cikin mutane 25 da suka rasa rayukansu a hatsarin haka kuma ga iyalan dukkan wadanda suka rasa rayukansu a wannan hatsarin jirgin sama mai ban tausayi” in ji Gwamna Eno.
KARANTA KUMA:http://Kungiya ta yi Makokin Wadanda suka Rasu a Hatsarin Jirgin Sama na NAF
Gwamnan ya kuma nuna goyon bayansa ga Rundunar Sojin Najeriya da iyalan wadanda suka rasu yana mai cewa Jihar Akwa Ibom na tare da su a wannan lokaci na bakin ciki.
Ya bi sahun Babban Kwamandan Rundunar Sojin Najeriya Shugaba Bola Tinubu—wanda ya ayyana kwanaki uku na makokin kasa—wajen nuna alhini ga iyalan wadanda suka rasu.
Gwamna Eno ya yi addu’ar Allah Ya ba iyalan wadanda suka rasu da masoyansu hakuri da karfin gwiwa tare da yaba da gudunmawar da marigayan suka bayar a rayuwarsu.
“Allah Ya gafarta masu” in ji shi.



