Babu Barkewar Cutar Ebola A Kenya – Sakataren Lafiya

Ministan Lafiya na Kenya Aden Duale ya bayyana cewa kasar ba ta fuskantar barkewar cutar Ebola ba duk da cewa an samu mutum na farko da ya mutu sakamakon cutar.
Duale ya bayyana cewa hukumomin kiwon lafiya na daukar lamarin a matsayin wani abu da ya faru ga mutum daya tak ba bullar annoba a ko’ina ba yayin da suke kara kaimi wajen gano mutanen da suka yi mu’amala da mamacin.
Ya ce hukumomi sun gano mutane 57 da suka yi mu’amala da shi bayan sun kara wasu mutane biyu a kan mutane 55 da aka fara gano su.
A cewarsa an riga an gano mutane 10 daga cikin wadanda suka yi mu’amala da shi kuma an killace su a Asibitin ‘Yan Sanda na Kasa (National Police Service Hospital) da ke Nairobi inda ake sanya su ido kullum don ganin ko za su nuna alamun cutar.
KARANTA KUMA:http://Kenya ta tabbatar da bullar cutar Ebola ta farko da aka shigo da ita daga Congo
Duale ya ce ana kara kaimi wajen gano sauran mutanen da suka yi mu’amala da shi.
Ya bayyana cewa hukumomin kiwon lafiya sun bibiyi tafiyar majiyyacin daga Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ta Kampala Uganda zuwa Nairobi inda aka kwantar da shi a asibiti.
Jawabin ministan ya zo ne kwana guda bayan Kenya ta tabbatar da bullar cutar Ebola ta farko ga wani dan kasar Kenya da ke zaune a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo.
Majiyyacin ya rasu ne yayin da ake ba shi kulawa a wani asibiti da ke Nairobi.
Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ta sanar da bullar cutar Ebola a watan Mayu bayan an gano cutar a wani yanki mai nisa a gabashin Congo.



