Zambia da Amurka za su rattaba hannu kan yarjejeniyar kiwon lafiya ta shekaru biyar

Zambiya za ta sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru biyar ta tallafin lafiya da ta kai dala biliyan 1.5 da Amurka a ranar Alhamis, bayan warware damuwar da ake da ita kan raba bayanai na likitanci.
Ministan Lafiya Elijah Muchima ya ce a ranar Talata cewa yarjejeniyar za ta sa Amurka ta samar da dala biliyan 1.5 a fannin kiwon lafiya a cikin shekaru biyar yayin da Zambiya za ta bayar da gudummawar dala biliyan 2.1 ga shirye-shiryenta na kiwon lafiya.
Tattaunawa ta tsaya cak saboda damuwar Zambiya game da sirrin bayanai da rahotannin da ke cewa Amurka na son tallafin kiwon lafiya ya danganta da samun damar shiga ma’adanai masu mahimmanci.
Ministan ya ce “raba bayanai a karkashin yarjejeniyar za ta takaita ne ga bayanan da ake bukata don sa ido da kimanta shirye-shiryen kiwon lafiya da Amurka ke daukar nauyinsu.”
Muchima ya ce an cire wani sashe da ke bukatar Zambiya ta samar da samfuran likitanci ga marasa lafiya zuwa Amurka idan an buƙata daga yarjejeniyar.
Dangane da damuwar cewa tallafin kiwon lafiya yana da alaƙa da samun damar shiga ma’adanai masu mahimmanci Muchima ya ce “babu wani ambato game da ma’adanai masu mahimmanci a cikin yarjejeniyar lafiya.”
Ya kara da cewa bai san wata yarjejeniyar ma’adanai daban-daban da ake tattaunawa tsakanin Zambiya da Amurka ba.
Amurka babbar mai ba da tallafin kuɗi ne ga shirye-shiryen HIV/AIDS zazzabin cizon sauro da sauran shirye-shiryen kiwon lafiyar jama’a a Zambia babbar ƙasa mai samar da tagulla a Kudancin Afirka.
Ƙasashen Afirka da dama sun nuna damuwa game da buƙatar Amurka na samun damar samun bayanai na likita a matsayin sharaɗi don samun tallafin lafiya.
Kenya da Tanzania da Uganda sun sanya hannu kan irin wannan yarjejeniyar kiwon lafiya da Amurka a ƙarƙashin wata sabuwar hanyar Amurka ta ba da tallafin ƙasashen waje da nufin taimaka wa ƙasashen da ke karɓar tallafin su su koma dogaro da kansu.
Duk da haka Ghana da Zimbabwe sun yi watsi da irin wannan yarjejeniya saboda damuwa game da buƙatun raba bayanai.
Reuters/Ladan Nasidi.



