Fitattun LabaraiNajeriya

Shugaba Tinubu Ya Yi Nazarin Tsarin Tsaro Da kare kasa A Najeriya

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakuncin Ministan Tsaro Janar Christopher Gwabin Musa (Rtd.) a Fadar Shugaban Kasa da ke Legas domin yin bitar tsarin tsaron kasa da tsaron Najeriya.

Tattaunawar ta shafi ayyukan yaki da ta’addanci da na ‘yan fashi da makami bukatun ayyukan da ke gaba-gaba da dabarun tsaro tsakanin hukumomi.

An sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Ministan kan Harkokin Watsa Labarai Leah Katung-Babatunde ta fitar.

Taron ya kuma yi nazari kan shirye-shiryen tsaro na yanzu da kuma shawarwarin gyare-gyare da nufin “ƙarfafa kwarin gwiwar sojoji sabunta kayan aikin soja da inganta kayayyakin more rayuwa na soja a fadin kasar.”

KARANTA KUMA: Sabon Ministan Tsaro Ya Yi Alkawarin Gaggawa Kan Gyaran Dabaru

Shugaba Tinubu ya nuna gamsuwa da ci gaban da aka samu wajen kare al’ummomin da ke cikin mawuyacin hali kuma ya sake jaddada kudirin gwamnatinshi na tallafawa Ma’aikatar Tsaro.

Janar Musa ya yi wa Shugaban kasa bayani game da shirye-shiryen tsaro na yanzu, dabarun aiki da kuma sauye-sauyen da aka gabatar yayin da ya nuna godiyarshi ga ci gaba da jagorantar Shugaban da goyon bayansa ga rundunar tsaron Najeriya.

Ministan ya tabbatar da cewa Ma’aikatar Tsaro ta ci gaba da jajircewa wajen aiwatar da umarninta cikin jajircewa da aminci.

Wannan yarjejeniya ta kasance wani bangare na ci gaba da gabatar da bayanai kan tsaro da kuma zaman daidaita manufofi da Shugaban kasa ke yi da manyan jami’an gwamnati yayin da gwamnati ke aiki don magance kalubalen tsaro da tattalin arziki a fadin kasar.

 

Laan Nasidi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button