Wasanni

Super Eagles Sun Fara Atisaye Gabanin Wasan Sada Zumunta Da Rasha.

Kungiyar Super Eagles ta gudanar da atisayenta na farko a birnin Nizhny Novgorod yayin da take shirin fafatawa a wasan sada zumunta na kasa da kasa da za a yi ranar Talata tsakaninta da babbar tawagar kasar Rasha ta maza.

Jerin ‘yan wasa 17 da suka yi atisayen ranar Asabar sun hada da Moses Simon (wanda ya buga wa kasar wasanni sama da 100) mai tsaron gida Stanley Nwabali masu tsaron baya Benjamin Fredricks da Emmanuel Fernandez da kuma ‘yan wasan gaba Kelechi Iheanacho da Akor Adams.

Kungiyar za ta sake gudanar da wasu atisayen guda biyu a ranakun Lahadi da Litinin kafin karawar da za a yi a filin wasa na Nizhny Novgorod a yammacin ranar Talata.

Karanta kuma: Super Eagles Ba Za Ta Yi Watsi da Karfin Guinea-Bissau Ba In ji Chelle

Wasan Sada Zumunta na Kasa da Kasa: Super Eagles Za Ta Kara da Rasha

‘Yan wasa da jami’an kungiyar sun yi tafiya ne ta jiragen sama na Turkish Airlines da Ethiopian Airlines inda suka bi ta biranen Istanbul da Addis Ababa kafin su isa Moscow sannan aka tafi da su Nizhny Novgorod ta jirgin sama.

A ranar 6 ga watan Yunin bara Rasha da Najeriya sun tashi kunnen doki 1-1 a filin wasa na Luzhniki da ke Moscow inda Rasha ta fara cin kwallo ta hannun dan wasan baya Semi Ajayi (wanda ya zura kwallo a ragar kungiyarsa bisa kuskure) kafin daga bisani Tolu Arokodare ya farke kwallon tare da daidaita sakamakon wasan ga Super Eagles.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button