Hare-haren Saman Rasha Sun Bugi Wata Gada Da Wani Ginin Gidaje A Kyiv

Magajin garin Kyiv babban birnin Ukraine Vitali Klitschko ya bayyana a ranar Juma’a cewa hare-haren jiragen saman Rasha sun sake afkawa gadar Southern Bridge da ke birnin.
Klitschko ya ce hare-haren sun lalata gadar da wasu sassan birnin tare da haifar da gobara a benayen saman wani ginin gidajen zama.
An dakatar da zirga-zirgar ababen hawa a kan gadar Southern Bridge da kuma gadar Paton Bridge da ke kusa da ita a bangarorin biyu yayin da hukumomi ke jagorantar direbobi zuwa wasu hanyoyin daban.
Wadannan hare-haren na baya-bayan nan sun zo ne kwana guda bayan da jiragen saman Rasha marasa matuki suka afkawa wata makaranta da gadar Southern Bridge lamarin da ya haifar da gobara a Kyiv.
KARANTA KUMA: http://Harin Rasha a Babban Birnin Ukraine Ya Jikkata Mutane 10
A dayan bangaren kuma jiragen saman Ukraine marasa matuki sun kai hari kan wuraren masana’antu a birnin Volgograd na Rasha inda ake da babban wurin tace man fetur a cewar gwamnan yankin.
Gwamnan ya ce hare-haren sun haifar da gobara a wani wurin masana’antu tare da jikkata mutum daya bayan da wani jirgi mara matuki ya bugi wani ginin gidajen zama.
Ukraine ta sha kai hare-hare kan wuraren tace man fetur da sauran wuraren samar da makamashi na Rasha a lokacin yakin. Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa hare-haren sun rage yawan kayayyaki da ayyukan da kasar ke samarwa (GDP) da kashi 1 cikin dari yayin da katsewar samar da man fetur ya haifar da dogayen layuka a gidajen mai a wasu yankuna.



