AfirkaKiwon Lafiya

Yawan Wadanda Suka Mutu Sanadiyyar Cutar Ebola A DRC Ya Haura 4,000

Bayanan gwamnati da aka fitar a ranar Juma’a sun nuna cewa adadin wadanda suka mutu sakamakon barkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ya kai 4,018 yayin da adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 8,300 a larduna bakwai.

Wannan annoba wadda nau’in kwayar cutar Ebola na Bundibugyo ke haifarwa ita ce mafi muni a tarihin kasar inda ta zarce annobar da ta faru tsakanin shekarun 2018 zuwa 2020.

Sabbin alkaluman sun nuna cewa fiye da marasa lafiya 2,000 ne suka warke daga cutar.

A yanzu, wannan ita ce annobar Ebola ta biyu mafi muni a tarihi bayan wadda ta faru a Yammacin Afirka tsakanin shekarun 2014 zuwa 2016 wadda ta shafi mutane sama da 28,600 tare da yin sanadiyyar mutuwar fiye da mutane 11,000 a kasashen Guinea Liberia da Sierra Leone.

A watan da ya gabata gwamnatin Congo da Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana cewa yaduwar cutar na raguwa a wasu sassan lardin Ituri inda annobar ta fara.

Sai dai kwayar cutar na ci gaba da yaduwa cikin sauri a gabashin Congo ciki har da lardin North Kivu mai makwabtaka da yankin.

Lardin South Ubangi dake arewa maso yammacin Congo ya zama lardi na bakwai da ya bayar da rahoton barkewar cutar a watan da ya gabata bayan mutuwar wani mutum da ya yi tafiya daga gabashin Congo sakamakon kamuwa da kwayar cutar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button