Afirka

Za A Binne Tsohon Firayim Ministan Guinea Touré A ƙasashen Waje

Za a binne tsohon Firayim Ministan Guinea Sidya Touré wanda ya rasu a birnin Paris yana da shekaru 81 a duniya a kasar Ivory Coast inda ya zauna a gudun hijira tun bayan juyin mulkin soji na shekarar 2021.

A cewar gidan rediyon Radio France Internationale (RFI) Touré ya rasu ne a makon da ya gabata a Paris inda yake karbar kulawar likita bayan ya yi rashin lafiya a birnin Abidjan.

Ya zauna an Ivory Coast tun watan Satumbar 2021 bayan juyin mulkin soji da ya hambarar da Shugaba Alpha Condé tare da kawo Janar Mamadi Doumbouya kan karagar mulki.

Touré ya rike mukamin Firayim Ministan Guinea daga watan Yulin 1996 zuwa Maris na 1999 a karkashin shugaban kasar na wancan lokacin Lansana Conté wanda ya mulki kasar daga 1984 zuwa 2008.

A lokacin da yake kan mukamin ya yi kokarin aiwatar da sauye-sauye a fannin gudanarwa da tattalin arziki tare da neman karfafa dangantakar Guinea da cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya.

Bayan ya sauka daga mukaminsa Touré ya ci gaba da kasancewa fitaccen dan adawa a matsayin shugaban jam’iyyar Union of Republican Forces (UFR) daya daga cikin manyan jam’iyyun adawa na Guinea.

Jam’iyyar UFR na daya daga cikin jam’iyyun siyasa 40 da hukumomi suka rusa a watan Maris a wani bangare na matakan takaita ayyukan siyasa da aka dauka a kasar.

Jam’iyyar ta bayyana cewa yin jana’izarsa a Guinea abu ne da “ba zai yiwu ba” saboda “wulakancin” da Touré ya fuskanta “a hannun hukumomin Guinea.”

Ana sa ran gawar Touré za ta isa birnin Abidjan a ranar Juma’a kafin a gudanar da jana’izarsa a Ivory Coast.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button