Gwamnan Jihar Kwara Ya Yi Kira Ga Zaman Lafiya Da Hadin Kai Yayin Bikin Samun ‘Yancin Kai

Gwamnan Jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya yi kira ga dukkan ‘yan Najeriya da su dauki Ranar Samun ‘Yancin Kai a matsayin lokacin yin nazari kan juriyarmu bambance-bambancen al’adu da kuma hadin kanmu a matsayin kasa daya tare da sabunta alkawarin gina kasar da muke burin samu.
Yayin jawabi a Ilorin a wajen bikin cika shekaru 66 da Najeriya ta samu ‘yancin kai Gwamnan ya yaba wa ‘yan kasa bisa jaruntaka kwazon kasuwanci kirkire-kirkire da kuma kudurin da suka nuna duk da kalubalen da ake fuskanta.
Yayin da yake taya Shugaba Bola Ahmed Tinubu da dukkan ‘yan kasa murnar wannan rana Gwamnan ya yi kira ga jama’a da su guji tashin hankali aikata laifuka da kalaman kiyayya tare da rungumar zaman lafiya da tsaron bai-daya.
KARANTA KUMA: Bikin Cika Shekaru 66: Malamin Addini Ya Yi Kira ga Hadin Kai da Gina Kasa
“A yau yayin da muke bikin cika shekaru 66 da samun ‘yancin kan Najeriya ina taya al’ummar Jihar Kwara da ‘yan Najeriya murna ko suna gida ko a kasashen waje” in ji shi.
“Ranar Samun ‘Yancin Kai lokaci ne na bikin nuna juriya bambance-bambancen al’adu da hadin kanmu tare da sabunta alkawarin gina Najeriya irin wacce muke burin samu.
“Duk da kalubalen da muke fuskanta ‘yan Najeriya na ci gaba da nuna jaruntaka kwazon kasuwanci kirkire-kirkire da kuduri wadanda su ne manyan dukiyoyin kasarmu.”
AbdulRazaq ya yi amfani da damar wajen bayyana wasu daga cikin nasarorin gwamnatinsa da suka shafi rayuwar Jama’a musamman a fannonin ilimi noma kiwon lafiya da kuma gyaran birane.
Ya bayyana cewa gwamnati na ci gaba da karfafa harkokin noma da inganta rayuwar manoma ta hanyar shirye-shirye irin su Kwara SAPZ L-PRES da sauran matakan tallafi wadanda suka samar da karin damammaki ga manoma sama da 100,000 tare da samar da cibiyoyin harkokin noma hanyoyin karkara da tallafin amfani da na’urorin zamani a harkar noma.
“A Kwara gwamnatinmu ta mayar da hankali kan inganta rayuwar jama’a. A fannin ilimi shirin KwaraLEARN ya horar da malamai dubbai ya samar da littattafan karatu da kayan aiki sama da miliyan 1.2 tare da gabatar da na’urorin zamani na dijital a makarantun firamare sama da 1,500” in ji Gwamnan.
“Mun gina azuzuwa sama da 2,000, mun dauki malamai kusan 9,000 aiki mun kafa Jami’ar Ilimi ta Jihar Kwara (Kwara State University of Education) mun soke biyan kudaden gudummawar PTA a makarantun firamare na gwamnati, tare da dawo da damar samun tallafin hukumar UBEC.”
“A fannin kiwon lafiya a yanzu jihar Kwara ce ke da mafi karancin yawan mace-macen yara ‘yan kasa da shekaru biyar a Najeriya inda ake samun kimanin mace-mace 14 a cikin kowane haihuwa 1,000 na yara masu rai.An gyara an samar da kayan aiki tare da sanya tsarin amfani da hasken rana a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko sama da 200 yayin da aka inganta Babban Asibitin Ilorin zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Kwara.”
Kafin ya gabatar da jawabinsa Gwamnan ya duba jerin gwano na jami’an tsaro da kuma daliban makaranta da suka gudanar da jerin gwano na musamman.
Daga cikin manyan mutanen da suka halarci taron akwai Mataimakin Gwamna Mista Kayode Alabi Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kwara kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC Rt. Hon. Salihu Yakubu Danladi abokin takararsa Hon. Seun Oguniyi ADATO sauran ‘yan majalisar dokokin jihar mambobin majalisar zartarwa da kuma dalibai daga wasu zababbun makarantu.
Babban abin da ya dauki hankali a wajen taron shi ne yadda Gwamna ya yanka kek din bikin samun ‘yancin kai tare da rakiyar Mataimakin Gwamna Kakakin Majalisa da sauran manyan mutane.



