Najeriya

Najeriya Ta Samu Guraben Aikin Hajji 60,000 Na Shekarar 2027

Najeriya ta samu karin guraben aikin Hajji guda 10,000 daga kasar Saudiyya domin aikin Hajji na shekarar 2027 lamarin da ya kara yawan guraben da aka ware wa kasar daga 50,000 zuwa 60,000.

Shugaban Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) Ismail Yusuf ne ya sanar da hakan a yayin Babban Taron Majalisar Kololuwa ta Harkokin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) a harabar Babban Masallacin Kasa da ke Abuja.

Yusuf ya bayyana cewa an ware guraben da aka samu karin su wadanda yawansu ya kai 7,500 ga hukumomi da kwamitocin kula da jin dadin mahajjata na jihohi yayin da aka ware sauran 2,500 ga manyan kamfanonin shirya tafiye-tafiyen Hajji guda bakwai da ke da lasisi.

KARANTA KUMA:http://Aikin Hajji na 2026: NAHCON ta samu amincewar Saudiyya kan cibiyoyin kiwon lafiya

Ya yi kira ga sarakunan gargajiya, hukumomin kula da jin dadin mahajjata da sauran masu ruwa da tsaki da su karfafa gwiwar masu niyyar zuwa aikin Hajji su yi rajista da wuri yana mai jaddada cewa bin ka’idojin lokacin rajista yana da matukar muhimmanci ga shirye-shiryen Najeriya na gudanar da aikin Hajji.

A cewarshi yin rajista da wuri zai kuma taimaka wajen daidaita shirye-shiryen aikin Hajji na Najeriya da tsarin gudanar da aikin Hajji na zamani na na’ura mai kwakwalwa da kuma ka’idojin gudanarwa na kasar Saudiyya.

Yusuf ya yaba wa gwamnatin Najeriya da hukumomin Saudiyya bisa ci gaba da ba da hadin kai da goyon baya ga mahajjatan Najeriya inda ya ce karin guraben da aka samu ya nuna kyakkyawar alaka da ke tsakanin kasashen biyu.

Ya ba da tabbacin cewa za a gudanar da harkokin wadannan sabbin guraben cikin gaskiya da kuma bin dokoki da ka’idojin Najeriya da Saudiyya.

Har ila yau shugaban na NAHCON ya sake jaddada kudirin hukumar na ganin an gudanar da aikin Hajji cikin sauki da kuma farashi mai sauki tare da tabbatar da ingancin ayyuka gaskiya da rikon amana da kuma ingantaccen tsarin gudanarwa.

Babban taron na NSCIA ya kuma kunshi addu’o’in kasa da malaman addinin Musulunci manyan limamai da sarakunan gargajiya daga dukkan yankuna shida na Najeriya suka halarta.

Mahalarta taron sun yi addu’ar samun zaman lafiya, kwanciyar hankalin tattalin arziki tsaron kasa da kuma neman shiriya daga Allah ga shugabannin kasar.

Yusuf ya kara da ba da tabbacin cewa NAHCON za ta ci gaba da yin aiki tare da hukumomin Saudiyya da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da gudanar da aikin Hajji na 2027 cikin tsari mai kyau tare da kare jin dadi da muradun mahajjatan Najeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button