Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 56 A Indiya Da Kuma 14 A Nepal

Hukumomi sun bayar da rahoton cewa mutane 56 a Indiya da 14 a Nepal sun rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa da suka biyo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da guguwa yayin da ake ci gaba da neman wasu mutane 11 da suka bata tare da yin gargadin cewa akwai yiwuwar sake samun ambaliyar ruwa ta kwatsam.
Jihar Uttar Pradesh ta arewacin Indiya ta samu ruwan sama mai yawan milimita 66.5 tsakanin ranar 25 ga watan Satumba da safiyar ranar 27 ga watan Satumba idan aka kwatanta da adadin milimita 7.6 da aka saba samu a wannan lokacin kamar yadda Hrishikesh Bhaskar Yashod kwamishinan kula da ayyukan agaji na jihar ya bayyana a ranar Lahadi.
Rahotanni sun nuna cewa baya ga mutuwar mutane 56 an samu mutane 46 da suka jikkata tare da lalacewar gidaje sama da 1,000.
Hukumomin Nepal sun yi gargadin yiwuwar samun ambaliyar ruwa ta kwatsam a gundumomi 49 daga cikin gundumomi 77 na kasar inda fiye da rabinsu ke fuskantar babban hadarin ambaliyar ruwa ko ambaliya ta kwatsam yayin da matakin ruwa a manyan koguna da rassan kogunan ke ci gaba da hawa.
KARANTA KUMA: Nepal ta gudanar da ranar makoki ta karshe
Kakakin Hukumar Kula da Rage Hadarin Bala’i da Gudanar da Ayyukan Agaji ta Kasa Shanti Mahat ya ce yankunan Rasuwa da Nuwakot—wadanda ambaliyar ruwa mai muni ta watan da ya gabata ta shafa inda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 1,450 tare da barin dubban mutane a cikin halin bacewa—ya kamata su ci gaba da kasancewa cikin shiri amma a halin yanzu ba a dauke su a matsayin yankuna masu matukar hadari ba.
An samu katsewar wutar lantarki gaba daya a gundumomin Manang Mustang Myagdi da Baglung yayin da hukumomi ke kokarin dawo da wutar a cewar jami’an ma’aikatar makamashi.
Ministan Albarkatun Ruwa da Makamashi Biraj Bhakta Shrestha ya bayyana cewa ambaliyar kogin Rahuganga ta lalata tsari da hasumiyoyin layin watsa wutar lantarki na wani aikin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da ruwa mai karfin megawatt 40.
Hukumar Kula da Ruwa ta Tsakiya ta Indiya ta bayyana cewa tashoshi 30 masu sa ido kan koguna a jihohi bakwai sun nuna cewa yanayin yana da matukar tsanani.
Manyan koguna da dama ciki har da Ganga Gandak Kosi Bagmati da Narmada sun haura matakin da ke nuna hadari.
Ministan Sadarwa na Nepal Bikram Timilsinha ya ce ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa sun kuma haifar da katsewar hanyoyin sadarwa a wasu sassan kasar Nepal bayan lalacewar igiyoyin sadarwa na zamani (optical fibres) da kuma tsarin samar da wutar lantarki.



