Tailan Ta Ayyana Bangkok A Matsayin Yankin Da Ke Fuskantar Bala’i Yayin Da Ambaliyar Ruwa Ke Karuwa.

Gwamnan Bangkok Chadchart Sittipunt ya ayyana babban birnin kasar Tailan a matsayin yankin da bala’i ya shafa bayan da mazauna birnin suka tashi suka ga ambaliyar ruwa ta mamaye wurare da dama tare da nutsar da wasu hanyoyi yayin da ake sa ran ci gaba da samun ruwan sama.
Bangkok ta fuskanci ruwan sama ba kakkautawa na tsawon fiye da sa’o’i 24 inda adadin ruwan ya zarce milimita 150 a wasu sassan birnin.
Hukumar kula da yanayi ta yi hasashen samun hadari tare da ruwan sama mai karfi ko ma mai tsananin karfi a karshen mako.
Sittipunt ya bayyana cewa halin da ake ciki “yana jefa rayuwar mutane cikin hadari tare da haifar da barna ga dukiyoyin jama’a da na masu zaman kansu.”
KARANTA KUMA: Nepal Na Neman Tallafin Kuɗi Na Duniya Domin Farfadowa Daga Ambaliyar Ruwa.
Gwamnati ta fitar da gargadin gaggawa ga mutanen da ke zaune kusa da magudanan ruwa inda ta bukace su da su mayar da kayansu zuwa wurare masu tsayi.
Ruwan ambaliya ya mamaye motoci, yayin da jami’an agajin gaggawa suka bayar da tallafi.
Hukumar birnin Bangkok ta sanar da bude cibiyar karbar mutanen da aka kwashe daga wuraren da ambaliyar ta shafa.



