Siyasa

Matan Gombe Na Neman Alkawari Daga Masu Son Tsayawa Takara Gabanin Zaben 2027

Kungiyoyin mata a Jihar Gombe sun fara tattara masu ruwa da tsaki gabanin babban zaben shekarar 2027 inda suke neman alkawari daga ‘yan takarar siyasa kan magance matsalolin da ke shafar mata da ‘yan mata a fadin jihar.

Wannan shiri wanda aka fi sani da “Gombe Women Agenda” ya hada kungiyoyin mata sama da 100 da aka yi wa rajista a karkashin wata kungiya ta bai-daya da nufin samar da takardar bukatu ta bai-daya da kuma tattaunawa da ‘yan siyasa kan batutuwan da suka shafi mata.

Da yake jawabi a wani taron masu ruwa da tsaki a Gombe mai shirya taron na “Gombe Women Agenda” Mista Ibrahim Yusuf ya bayyana cewa an tsara shirin ne domin tabbatar da cewa an sanya batutuwan da suka shafi mata cikin tsare-tsare da manufofin ‘yan siyasar da ke neman mukamai a zaben 2027.

A cewar Yusuf shirin yana mayar da hankali ne wajen hada kai da daidaita bukatun mata gano manyan matsaloli da kuma gabatar da shawarwari da ‘yan takara za su iya daukar alkawarin aiwatarwa.

Ya ce masu shirya taron sun sanya maza masu ruwa da tsaki tare da wakilan kungiyoyin Musulunci da na Kirista, cikin shirin da gangan saboda ba za a iya samun ci gaban mata ta hanyar mata su kadai ba.

“Muna ganin ba daidai ba ne a ce za a tuntuɓi ‘yan siyasa kai tsaye ba tare da samun goyon bayan maza ba” in ji Mista Yusuf.

Ya bayyana cewa mahalarta taron sun yi nazari tare da tantance takardar don tabbatar da cewa ta yi daidai da bukatun al’umma baki daya, kuma ba ta saba wa koyarwar addini ko al’adu ba.

Mista Yusuf ya ce daga cikin muhimman batutuwan da ke cikin shirin akwai ilimin ‘yan mata mutuwar mata yayin haihuwa karfafa mata ta fuskar tattalin arziki da kuma kara shigar mata cikin harkokin siyasa da tsarin yanke shawara.

Ya ce mata na taka muhimmiyar rawa a fannin tattalin arziki amma sau da yawa ba a ba su cancantaccen yabo ko kulawa kan gudummawar da suke bayarwa ba.

Mista Yusuf ya kuma yi nuni da cewa magance matsalolin mata zai yi tasiri mai fadi ga iyalai da al’ummomi kasancewar mata ne galibi ke daukar nauyin kula da yara, maza da kuma masu rauni ciki har da masu nakasa.

Ya ce saboda haka shirin na neman magance kuskuren fahimtar al’adu da fassarar addini wadanda masu shirya taron ke ganin za su iya takaita shigar mata cikin harkokin ci gaba da siyasa.

Mista Yusuf ya ce an sanya shugabannin addini da sauran masu ruwa da tsaki masu tasiri cikin shirin ne domin taimakawa wajen magance irin wadannan matsaloli da kuma samun karin goyon baya ga shirin.

Ya ce shirin wanda za a gabatar wa ‘yan takarar jam’iyyu na zaben 2027 ya kunshi manyan ginshikai 10 da shawarwari kusan 20 wadanda suke shirin gabatarwa ga masu neman mukaman siyasa kafin zaben na 2027.

Mista Yusuf ya bayyana cewa ana sa ran kaddamar da shirin a bainar jama’a a watan Satumba.

Sai dai ya lura cewa kalubalen da suka shafi samar da kudade na iya shafar lokacin da aka tsara don gudanar da hakan.

Ya bayyana cewa daga baya za a samar da kwafin takardun ga jama’a da kuma masu ruwa da tsaki a fannin siyasa domin samun alkawuran aiwatar da shawarwarin da ke cikinsu.

Sakatariyar kungiyar ‘Gombe Women Agenda’ Ruth Abner ta bayyana cewa masu ruwa da tsaki suna da matukar muhimmanci wajen nasarar wannan shiri saboda haka aka fahimci cewa cimma manufofin shirin zai bukaci hadin gwiwa da ta wuce iyakar kungiyoyin mata kadai.

“Muna bukatar hadin gwiwarsu kafin mu iya cimma wannan manufa” in ji Mrs. Abner.

Ta bayyana cewa kungiyar ta kunshi kungiyoyin mata sama da 100 da aka yi wa rajista wadanda mambobinsu ke neman samun karin wakilci da kuma shiga cikin harkokin yanke shawara.

Mrs. Abner ta ce mata na fuskantar kalubale da dama wadanda ba za a iya magance su yadda ya kamata ta hanyar kokarin kungiya daya ko biyu ba lamarin da ya sa kungiyoyin suka hada karfi wuri guda domin kara karfin muryoyinsu.

Ta kuma yi nuni da cikas da ke hana mata shiga harkokin zabe ciki har da rashin isasshen goyon baya daga maza rashin tsaro da kuma rikice-rikice ko tashin hankali a wuraren kada kuri’a.

A cewarta yana da matukar muhimmanci a samar da yanayi mai cike da tsaro domin bai wa mata damar shiga harkokin zabe sosai ko a matsayin masu kada kuri’a ko kuma a matsayin ‘yan takara.

Masu shirya taron sun bayyana cewa babban burinsu shi ne ganin an samu ci gaba mai ma’ana wajen kula da batutuwan da suka shafi mata, da kuma sanya su cikin harkokin yanke shawara da inganta rayuwarsu ta fuskar zamantakewa da tattalin arziki kafin da kuma bayan zaben shekarar 2027.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button