Wasanni

Ronaldo Nason Cimma Burin Zura Kwallo Ta 1000 A Rayuwarsa Ta Kwallon Kafa.

Cristiano Ronaldo ya sa a gaba burin cin kwallaye 1000 a rayuwarsa ta kwallon kafa kafin ya yi ritaya.

Kyaftin din tawagar Fotugal mai shekaru 41 yayin da yake jawabi a babban dandalin taron ‘Portugal Football Summit’ a ranar Laraba  gabanin wasan gasar UEFA Nations League da za su buga da Wales a ranar Alhamis  ya bayyana cewa har yanzu yana da abubuwa da yawa da zai iya bai wa kasarsa yayin da Jorge Jesus ke shirin jagorantar wasansa na farko a matsayin kociyan tawagar kasar.

Jesus ya maye gurbin Roberto Martinez ne bayan da tafiyar Fotugal a gasar cin kofin duniya ta kare cikin takaici a matakin zagayen kungiyoyi 16 inda suka sha kashi a hannun Sifaniya wadda daga bisani ta lashe gasar.

A yanzu Ronaldo yana da kwallaye 979 a tarihin aikinsa 833 a kungiyoyi da kuma 146 a tawagar Fotugal  wanda ke nufin ya rage masa kwallaye 21 kacal kafin ya kai ga adadin kwallaye 1000 da ya bayyana a fili cewa yana son cimmawa. Lokacin da aka tambaye shi ko wanne ya fi muhimmanci a tsakanin lashe gasar Nations League ko kuma cimma wannan adadi mai lambobi hudu sai ya yi murmushi tare da zabar duka biyun.

“Burina shi ne cimma duka biyun  kaiwa ga cin kwallaye 1000 da kuma ganin tawagar kasar ta yi nasarar lashe wannan gasa ta Nations League” in ji Ronaldo a taron ‘Portugal Football Summit’ da aka gudanar a hedkwatar hukumar kwallon kafar Portugal da ke wajen birnin Lisbon.

“Wannan sabon zamani ne tare da koci Jorge Jesus wanda dukkanmu muka san shi sosai ina fatan komai ya tafi masa da kyau.”

Karanta kuma: Cristiano Ronaldo Ya Ce Shekarar Da Ke Tafe Na Iya Zama Ta ƙarshe A Gare Shi

Sifen Ta kawo ƙarshen Burin Ronaldo Na Lashe Kofin Duniya Ta Kuma Tsallake Zuwa Matakin Daf Da Na Kusa Da Na ƙarshe

Ronaldo ya bayyana cewa cimma burin zura kwallaye 1000 a tawagar Fotugal zai zama “abin da zai cika ni’imar nasarar”.
“Zura kwallona ta 1000 a tawagar kasata zai zama kololuwar wani abu  wato labari mai dadi” in ji shi. “Ba zai zama karshen komai ba amma zai zama labari mai dadi.”

Sai dai Ronaldo ya jaddada cewa ba wai ya maida wannan burin a matsayin abin da ya mamaye tunaninsa gaba daya ba ne.

“Na riga na bayyana cewa ina son cimma hakan, kuma zan cimma shi” in ji shi. “Shin wani abu ne da ya zama kamar jaraba ko tsananin sha’awa? A’a… Abin da ya rage kawai shi ne jin dadin rayuwa da kuma jin dadin kowace rana.”

Ronaldo ya amince cewa ya yi tunanin makomarsa a tawagar kasar bayan fitar Fotugal daga gasar cin kofin duniya, amma ya ce tattaunawar da ya yi da hukumar kwallon kafa ta Portugal da kuma Jesus ta gamsar da shi ya ci gaba.

Da aka tambaye shi game da yin ritaya Ronaldo ya ki bayyana takamaiman lokacin da zai kawo karshen aikinsa na kwallon kafa.

“Na koyi wani abu tun lokacin da na shiga shekarun karshe na 30 wato in rayu a halin yanzu ba tare da damuwa da abin da zai faru gobe ba” in ji shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button