Mataimakin Shugaban Kasa Shettima Ya Shiga Cikin Shugabannin Duniya A Wajen Bude Taron Majalisar Dinkin Duniya Karo na 81.

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya shiga sahun shugabannin duniya wajen bude taron muhawara na babban zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 81 (UNGA) a hedkwatar majalisar da ke birnin New York.
Mataimakin Shugaban Kasa Shettima wanda ke wakiltar Shugaba Bola Tinubu tare da jagorantar tawagar Najeriya a wannan taro na duniya ya halarci liyafar karin kumallo ta maraba da aka shirya musamman ga shugabannin tawagogi da matansu wadda Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya karbi bakuncinta.
Mataimakin Shugaban Kasar ya isa zauren taron ne tare da Gwamnoni Dauda Lawal na Jihar Zamfara AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara da kuma Siminalayi Fubara na Jihar Ribas.
KARANTA KUMA: Mataimakin Shugaban Kasa Shettima Ya Samu Bayanai Kan Muhimman Batutuwan Taron Majalisar Dinkin Duniya Na 81 (UNGA)

Har ila yau cikin tawagar Najeriya akwai Ministan Tsaro Janar mai ritaya Christopher Musa Ministan Harkokin Waje Bianca Odumegwu-Ojukwu Wakilin Najeriya na Dindindin a Majalisar Dinkin Duniya Sanata Jimoh Ibrahim da sauran manyan jami’an gwamnati.
An bude babban taron tattaunawa na Majalisar Dinkin Duniya wanda ake gudanarwa daga ranar 22 zuwa 28 ga watan Satumba karkashin taken “Maido da amincewa da tafiyar da sauye-sauye: Majalisar Dinkin Duniya mai samar da sakamako ga kowa“tare da jawabin Sakatare-Janar na Majalisar António Guterres da kuma jawabai daga shugabannin kasashen duniya ciki har da Shugaban Brazil Luiz Inácio Lula da Silva da Shugaban Amurka Donald Trump.

An tsara Mataimakin Shugaban Kasa Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya a gaban Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya a ranar Alhamis 24 ga watan Satumba inda zai bayyana matsayin kasar game da muhimman batutuwan duniya da kuma muhimman abubuwan da Shugaba Tinubu ya sa a gaba kamar gyare-gyare a hukumomin duniya ci gaba mai dorewa zaman lafiya da tsaro matakan tinkarar sauyin yanayi da kuma samar da tsarin tattalin arzikin duniya mai adalci.
Jim kadan bayan kammala zaman bude taron Mataimakin Shugaban Kasar ya kuma ziyarci ginin ‘Nigeria House’ da ke birnin New York.

Mataimakin Shugaban Ƙasa zai kuma halarci wasu manyan ayyuka da kuma wasu ayyuka na haɗin gwiwa a lokacin makon UNGA yayin da Najeriya ke ci gaba da inganta muradun ƙasa da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa da abokan hulɗa na ƙasashen duniya.



