Duniya

Shugabannin Tsaro Na NATO Sun Zabi Carsten Breuer A Matsayin Shugaba

An zabi Janar Carsten Breuer babban hafsan sojin kasar Jamus a matsayin shugaban Kwamitin Soji na kungiyar NATO wanda shi ne babban matsayin jagorancin soji a kungiyar.

Kasashe 32 mambobin NATO ne suka zabi Breuer a matsayin shugaba mai zuwa yayin wani taro a Copenhagen kamar yadda shugaban kwamitin mai ci yanzu Admiral Giuseppe Cavo Dragone na Italiya ya bayyana a shafinsa na X.

Breuer zai karbi mukamin a lokacin bazara mai zuwa inda zai maye gurbin Dragone.

“Kwarewarka wajen yanke hukunci kan ayyukan soji da zurfin sanin da kake da shi game da wannan kungiya da kuma yadda ka jagoranci rundunar sojin Jamus za su amfani NATO sosai” in ji Dragone.

“Shugabannin soji sun dora maka amana a wannan lokaci mai matukar muhimmanci ga tsaron yankin Turai da Atlantic” ya kara da cewa.

Kwamitin Soji yana ba wa shugabannin siyasa na NATO shawara kan batutuwan da suka shafi soji inda shugaban kwamitin ke zama babban mai ba da shawara kan harkokin soji ga Babban Sakatare Mark Rutte.

KARANTA KUMA: Jirgin Yakin NATO Ya Harbo Jirgin Mara Matuki a Sararin Saman Romania

Breuer zai karbi mukamin ne a daidai lokacin da NATO ke sake duba yadda ake raba nauyin ayyukan tsaro tsakanin Amurka da kawayenta na Turai.

Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci kasashen Turai mambobin kungiyar da su dauki karin nauyi wajen tabbatar da tsaron nahiyar.

Gwamnatocin kasashen Turai sun kara kashe kudade a fannin tsaro sakamakon mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine a shekarar 2022 da kuma rashin tabbas game da irin gudummawar da Amurka za ta ci gaba da bayarwa ga NATO a nan gaba.

Jamus na daya daga cikin kasashen da suka fi kashe kudade a wannan fanni inda Berlin ke shirin ninka kudaden da take kashewa a fannin tsaro zuwa sama da Yuro biliyan 200 (dalar Amurka biliyan 230) nan da shekarar 2030.

Breuer mai shekaru 61 ya shiga rundunar sojin Jamus (Bundeswehr) a shekarar 1984 a matsayin jami’in tsaron sararin sama.

Daga baya ya halarci Kwalejin Horar da Manyan Hafsoshin Soji ta Amurka (US Army Command and General Staff College) da ke Fort Leavenworth Kansas da kuma horon manyan hafsoshin soji na Jamus a Hamburg. Ya yi aiki tare da Rundunar NATO ta Kasa da Kasa mai kula da Tsaro da Samar da Zaman Lafiya (ISAF) a Kabul a shekarar 2014.

Breuer ya samu lakabin “janar din shugaban gwamnati” (chancellor’s general) bayan da Olaf Scholz wanda shi ne shugaban gwamnati a lokacin ya nada shi shugaban kwamitin da ke kula da matakan da Jamus ta dauka wajen tunkarar annobar COVID-19 a shekarun 2021 da 2022.

Ana sa ran Lieutenant General Christian Freuding wanda shi ne babban hafsan sojin kasa na Jamus a yanzu zai maye gurbin Breuer a matsayin babban hafsan soji kafin karshen wannan shekara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button