Hare-Haren Sama Na Isra’ila Sun Kashe Falasdinawa Uku A Gaza.

Hare-haren sama da Isra’ila ta kai sun yi sanadiyyar mutuwar akalla Falasdinawa uku a yankin Gaza a ranar Asabar kamar yadda jami’an kiwon lafiya ma’aikatan lafiya da hukumar kare fararen hula suka bayyana.
Daya daga cikin hare-haren wanda ya faru kusa da sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia a arewacin Gaza ya yi sanadiyyar mutuwar Basir Al-Bursh dan Munir Al-Bursh wanda shi ne babban daraktan ma’aikatar lafiya ta yankin kamar yadda ma’aikatan lafiya da ‘yan uwa suka tabbatar.
Sojojin Isra’ila sun ce sun kai hari kan wasu ‘yan gwagwarmaya a ranar Asabar ciki har da Basir Al-Bursh amma ba su bayar da karin bayani ba. Kungiyar Hamas wacce ke tafiyar da harkokin Gaza ba ta yi tsokaci nan take ba.
Munir Al-Bursh ya rasa ‘yarsa a wani harin sama da Isra’ila ta kai a watan Disambar 2023 a cewar ‘yan uwa da ma’aikatan lafiya.Shi ma ya samu rauni a wancan harin.
A cikin wani bidiyo da ‘yan jarida suka samu an ga Al-Bursh yana dauke da gawar dansa wadda aka lullube ta da bargo yayin da masu jimami ke kai shi asibiti ta motar daukar marasa lafiya.
KARANTA KUMA: http://Hare-haren Sama na Isra’ila Sun Shafi Manyan Rumbunan Ajiya na Asibitin Gaza
A Asibitin Al-Shifa masu jimami sun taimaka wa Al-Bursh yayin da ‘yan uwa da sauran mutane suka taru domin nuna alhininsu.
A wani bangaren kuma wani hari ya kashe wani mutum a Shejaia gabashin birnin Gaza yayin da wani harin ya bugi wata mota a unguwar Sheikh Radwan ta birnin Gaza inda ya kashe mutum daya a cewar hukumar kare fararen hula da ma’aikatan lafiya.
Sojojin Isra’ila sun ce harin da aka kai Sheikh Radwan ya yi niyya ne kan wani dan gwagwarmayar Hamas.
Hukumomin Falasdinu sun ce an kashe mutane sama da 73,000 a yakin da Isra’ila ke gudanarwa a Gaza wanda ya fara bayan da mayakan da Hamas ke jagoranta suka kashe kimanin mutane 1,200 a kudancin Isra’ila a watan Oktoban 2023.
Yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Amurka ta shiga tsakani a bara ta tanadi sake gina Gaza nan gaba amma ba a samu ci gaba sosai ba yayin da masu tattaunawar ke ci gaba da rashin jituwa kan batun kwance damarar Hamas da kuma janye sojojin Isra’ila.
Jami’an kiwon lafiyar Gaza sun ce an kashe Falasdinawa sama da 1,300 wadanda yawancinsu fararen hula ne a yankin tun bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita bude wutar.Sojojin Isra’ila sun ce an kashe hudu daga cikin sojojinsu a wannan lokacin.



