Najeriya

Najeriya Da Faransa Sun Sake Jaddada Kudirinsu Na Karfafa Dangantaka Ta Bangarori Biyu.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya karbi bakuncin Shugaba Bola Ahmed Tinubu don cin abincin dare na sirri a Fadar Élysée da ke Paris. Wannan taron ya nuna dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Faransa da kuma jajircewarsu wajen karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Mai ba da shawara na musamman ga shugaban kasa kan bayanai da dabaru Mista Bayo Onanuga ya bayyana hakan a ranar Juma’a a cikin wani rubutu a shafinsa na X @aonanuga1956 yana mai cewa Shugaba Macron ya karbi shugaban Najeriya a daren Alhamis.

“Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya karbi Shugaba Bola Ahmed Tinubu don cin abincin dare na sirri ranar Alhamis da daddare a Fadar Élysée yana nuna dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Faransa da kuma jajircewarsu wajen karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu” in ji Onanuga.

KARANTA KUMA: http://Shugaba Tinubu Ya Nemi Zurfafa Hulɗar Tattalin Arziki Tsakanin Najeriya da Faransa

Wannan ganawar ta zo ne yayin da Shugaba Tinubu ke ci gaba da hutunsa na makonni uku a Turai wanda ya fara a ranar 30 ga Agusta 2026 a matsayin wani bangare na hutunsa na shekara-shekara.

Shugaban ya bar Abuja zuwa Landan Birtaniya inda ya shafe kashi na farko na hutun kafin ya tafi Faransa don mataki na biyu.


Shugaba Tinubu ya isa birnin Paris a ranar Lahadi inda jakadan Najeriya a Faransa Emmanuel Ayodele Oke ya tarbe shi.

Tun da farko fadar shugaban kasa ta bayyana hutun na tsawon makonni uku a matsayin hutu mai tattare da ayyuka inda Mista Onanuga ya bayyana cewa Shugaba Tinubu zai dawo Najeriya bayan kammala wannan lokacin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button