Najeriya

Gwamnatin Najeriya Za Ta Gudanar Da Taron Matasa Na Kasa A Watan Oktoba

Gwamnatin Najeriya na shirin gudanar da taron matasa na kasa (National Youth Confab) a watan Oktoba na shekarar 2026 inda ake sa ran samun wakilin matashi guda daga kowace mazabar zabe ta tarayya guda 360 na kasar tare da wakilai shida daga cikin ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje da sauran masu ruwa da tsaki.

Ministan raya matasa Comrade Ayodele Olawande ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar an Abuja babban birnin kasar ranar Alhamis domin sanar da fara shirin taron matasan na kasa.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar raya matasa Omolara Esan ta fitar.

Tare da taken “Next Gen Nigeria: Crafting Solutions Owning the Future” (Najeriya ta Sabuwar Zamani Samar da Mafita Mallakar Makoma) taron zai dauki tsawon makonni biyu zai fara ne da tattaunawa ta yanar gizo a fadin kasar sannan a biyo shi da taron fuska-da-fuska a Abuja.

A cewar Ministan “An tsara taron ne domin bai wa matasan Najeriya masu shekaru tsakanin 18 zuwa 35 damar bayyana damuwarsu gabatar da shawarwari kan manufofi da kuma bayar da gudummawar hanyoyin magance matsalolin da kasar ke fuskanta.”

KARANTA KUMA:http://CONFAB 2025: An bukaci matasan Najeriya su halarci taron da za a gudanar nan ba da jimawa ba

“Matasan Najeriya ba wai kawai shugabannin gobe ba ne su abokan tarayya ne wajen gina kasa a yau. Ra’ayoyinsu gogewarsu da kuma gudummawarsu suna da matukar muhimmanci ga ci gaban kasarmu” in ji shi.

Olawande ya bayyana cewa “tattaunawar a wannan taro za ta mayar da hankali ne kan muhimman fannoni ciki har da harkokin mulki da jagoranci; sauye-sauyen tattalin arziki da samar da ayyukan yi ilimi da bunkasa kwarewa fasaha da kirkire-kirkire sauyin yanayi da sauye-sauye a fannin makamashi da kuma zaman lafiya da tsaro a tsakanin al’umma.”

Ya jaddada cewa an shirya wannan shiri ne domin ya wuce matakin tattaunawa kawai zuwa ga samun sakamako mai amfani inda ya ce “Wannan dama ce ta sauraro tattaunawa hadin gwiwa da kuma sauya zance zuwa ga aiwatar da ayyuka na zahiri.”

Sakamakon da ake sa ran samu daga taron

Ministan ya kara da cewa za a samar da hanyoyin da suka hada da kwamitin musamman na masu ruwa da tsaki kan taron matasa tsarin auna tasirin taron da kuma tsarin sa ido da lissafi karkashin jagorancin matasa domin tabbatar da cewa an dore da sakamakon taron tare da aiwatar da su yadda ya kamata.

Ya yi kira ga matasan Najeriya a dukkan jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya da kuma wadanda ke kasashen waje da su shiga cikin tsarin sosai ta hanyar gabatar da ra’ayoyinsu shawarwari  da kuma abubuwan da suka fuskanta a rayuwa.

“Ma’aikatar Ci Gaban Matasa ta Tarayya a shirye take ta saurara kuma Gwamnatin Najeriya a shirye take ta tattauna da ku. Muna kira ga matasanmu da su fito su hada hannu da mu wajen tsara makomar Najeriya ta yau da ta gobe” in ji Olawande.

A jawabinta na maraba Sakatariyar Dindindin ta Ma’aikatar Ci Gaban Matasa ta Tarayya kuma Shugabar Kwamitin Taron Matasa na Kasa Dr. Maryam Ismaila Keshinro ta bayyana taron a matsayin muhimmiyar dama ta kara karfafa gudummawar matasa wajen ci gaban kasa. Shirin na kuma da nufin tabbatar da cewa matasan Najeriya suna taka rawar gani wajen samar da mafita ga matsalolin da ke shafar tsararsu.

Karɓar wannan tsari

Ta yi kira ga matasan Najeriya da masu ruwa da tsaki da su rungumi wannan tsari tare da bayar da gudummawa mai ma’ana domin cimma manufofin taron.

Haka kuma Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Kafofin Watsa Labarai na Zamani (Digital Media) Otega Ogra ya yaba wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu bisa wannan shiri tare da yaba wa mambobin Kwamitin Taron Matasa na Kasa bisa karɓar nauyin mayar da hangen nesan Shugaban Kasa game da matasan Najeriya zuwa wani shiri na kasa mai ma’ana.

Ogra ya bayyana cewa gwamnatin mai ci ta ci gaba da samar da damammaki ga matasan Najeriya domin su rike muhimman mukamai tare da bayar da gudummawa ga ci gaban kasa.

“Gwamnatin yanzu ta dora fatanta kan matasan Najeriya wajen ciyar da kasar gaba. Muna son ku gabatar da ra’ayoyinku a taron tattaunawar kasa. Kofarmu a bude take ga ‘yan Najeriya domin su bayyana yadda suke son kasar ta kasance” in ji shi.

Ogra ya yi kira ga matasan Najeriya da su yi amfani da damar da taron tattaunawar ya samar wajen gabatar da sabbin dabaru da hanyoyin magance matsaloli masu inganci wadanda za su iya ba da gudummawa wajen ci gaban kasar mai dorewa.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button