Najeriya

Majalisar Dokoki Ta Kasa Ta Fara Mataki Na Gaba Na Gyaran Kundin Tsarin Mulki.

Majalisar Dokoki ta Tarayya ta fara mataki na gaba na tsarin yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulki ta hanyar tura Kudirin Dokar Kwaskwarima ta Shida ga Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na shekarar 1999.

An tura kudirin zuwa Majalisun Dokoki na jihohi 36 na tarayya domin su yi nazari tare da amincewa da shi.

Sakataren Majalisar Dokoki ta Tarayya Mista Kamoru Ogunlana ya tura kudirin zuwa majalisun dokokin jihohin da abin ya shafa biyo bayan umarnin da shugabancin Majalisar Dokoki ta Tarayya ya bayar.

An dauki wannan mataki ne bisa tanadin Sashe na 9 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na shekarar 1999 (kamar yadda aka yi masa kwaskwarima) a ranar 16 ga watan Satumbar 2026.

Sashe na 9 na kundin tsarin mulkin ya tanadi cewa—tare da sauran sharudda—ba za a iya amincewa da kudirin dokar yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulki a ko wanne bangare na Majalisar Dokoki ta Tarayya ba sai idan majalisun dokoki na jihohi 36 na tarayya sun amince da shi ta hanyar kudiri inda dole ne a samu amincewar akalla kashi biyu bisa uku na wadannan majalisun jihohi.

Sakataren Majalisa ya bukaci Majalisun Dokoki na Jihohi da su bai wa kudirin dokar kulawar da ta dace bisa tsarin dokokinsu na aiki tare da sanar da Majalisar Dokoki ta Kasa game da matsayar da suka cimma bayan kammala nazarin kudirin.

KARANTA KUMA: Minista Ya Bukaci NITP Ta Bi Hanyar Yin Kwaskwarima Ga Kundin Tsarin Mulki.

An lura cewa Kundin Tsarin Mulki bai kayyade takamaiman lokacin da ya wajaba Majalisun Dokokin Jihohi su sanar da matsayarsu game da kudirin gyaran kundin tsarin mulkin ba.

“Duk da haka domin tabbatar da cewa an gudanar da tsarin gyaran kundin tsarin mulkin cikin tsari hadin kai da kuma kan lokaci ana sa ran Majalisun Dokokin Jihohi za su yi nazari kan kudirin tare da sanar da Majalisar Dokokin Tarayya matsayarsu a cikin kwanaki 30 bayan sun karbe shi.

“Domin karin bayani wannan wa’adin na kwanaki 30 tsari ne na gudanarwa kawai da ake sa ran bi ba kuma wa’adi ne da kundin tsarin mulki ya kayyade a matsayin tilas ba.

“Majalisar Dokokin Tarayya ta fahimci nauyin da kundin tsarin mulki ya dora wa Majalisun Dokokin Jihohi kuma tana mutunta ‘yancinsu wajen yin nazari kan kudirin. Manufar aika musu da kudirin ita ce don saukaka musu gudanar da aikinsu na tsarin mulki cikin tsari yayin wannan tsari” cewar Mista Ogunlana.

Ya bayyana cewa Majalisar Dokokin Tarayya ta kuduri aniyar tabbatar da cewa an gudanar da tsarin gyaran kundin tsarin mulkin bisa cikakken bin dokokin kundin tsarin mulkin tare da bin ka’idojin da suka dace hadin gwiwar hukumomi da kuma mutunta ayyukan majalisu a dukkan matakan gwamnati.

Ogunlana ya kara da cewa da zarar an karbi matsayar Majalisun Dokokin Jihohi Majalisar Dokokin Tarayya za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace kamar yadda tanade-tanaden kundin tsarin mulki suka tsara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button