Najeriya Da Thailand Sun Zurfafa Dangantaka A Fannonin Fasaha Da Noma

Najeriya da Thailand sun kuduri aniyar zurfafa dangantaka tsakaninsu a fannonin fasaha da noma da kasuwanci da makamashi mai sabuntawa, tare da sauran fannoni masu muhimmanci.
A wannan tsarin Najeriya na neman a sake duba yarjejeniyoyin hadin gwiwa da ke akwai tsakanin kasashen biyu tare da yin amfani da damar da Thailand ke da ita wajen aiwatar da fasahar matakin tsakiya a fannin noma da sauran fannoni masu nasaba da shi.

A daya bangaren kuma kasar Thailand na gabatar da shirin “Thailand-Africa Initiative” (Shirin Thailand da Afirka) da ke da nufin karfafa alaka tsakanin wannan kasa ta Asiya da muhimman kasashen Afirka ta fuskar hulda tsakanin al’ummomi da alakar tattalin arziki da kuma hadin gwiwa a fannin tattalin arziki musamman a bangaren noma.
Wadannan su ne muhimman batutuwan da aka tattauna a yayin ganawa tsakanin Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima da tawagar kasar Thailand karkashin jagorancin Mataimakin Firayim Minista kuma Ministan Harkokin Waje na kasar Yousef Hassan Khalawi.

Da yake jawabi a madadin Shugaba Bola Tinubu, Mataimakin Shugaban Kasa Shettima ya jinjina wa kyakkyawar alakar da ke tsakanin Najeriya da Thailand.
“Na yi imanin cewa ya kamata alakarmu ta wuce batun cinikin danyen mai noman shinkafa da sauran su kawai. Saboda haka akwai bukatar mu sake duba alakar kasashenmu biyu ta fuskar dabarun ci gaba.
“Najeriya babbar kasuwa ce. Akwai damammaki masu yawa na hadin gwiwa da zuba jari a fannonin noma da fasahar sadarwa (ICT) makamashi mai sabuntawa da ma’adanai da sannan muna da matasa da kuma karfin ma’aikata” in ji Mataimakin Shugaban Kasar.

Matsayi
Ya yi kira ga gwamnati da al’ummar kasar Thailand da su ci gaba da gudanar da harkokin kasuwanci da Najeriya la’akari da muhimmin matsayin da take da shi a nahiyar Afirka tare da fa’idar yawan al’ummarta da kuma dumbin albarkatun kasa da take da su.
Mataimakin Firayim Minista Khalawi wanda ke gudanar da ziyararsa ta farko a nahiyar Afirka ya yaba da sauye-sauyen da ake samu a Najeriya karkashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu inda ya bayyana kasar a matsayin ‘abokiyar hadin gwiwa mai muhimmanci ga Thailand da babbar murya a kasashen kudancin duniya da kuma kasa mai tasowa a fannin kasuwancin yanar gizo.’

Ya bayyana cewa Thailand na shirin kulla sabuwar yarjejeniyar hadin gwiwa da Afirka mai suna ‘Thailand-Africa Initiative’ (Shirin Thailand da Afirka) wadda aka tsara domin karfafa alakar tattalin arziki harkokin kasuwanci da kuma cudanyar al’umma tsakanin bangarorin biyu.
Mataimakin Firayim Minista ya bayyana cewa “Muhimmin bangare na wannan shiri shi ne inganta hadin gwiwar tattalin arziki musamman a fannin noma tare da yin amfani da karfin da Thailand ke da shi a fannonin samar da kiwon lafiya ga kowa da kuma yawon bude ido da sauran fannoni.”
Ya ce “A bangarenmu na Thailand mun yi imanin cewa Najeriya muhimmiyar abokiyar huldar kasashen biyu ce kuma kofa ce mai muhimmanci wajen karfafa alaka da nahiyar Afirka musamman ma yankin Yammacin Afirka.”
LADAN NASIDI.



