Shugaban Najeriya Ya Yi Watsi Da Kiran Da Ake Ni Na Mayar Da Tallafin Man Fetur

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sake jaddada matakin gwamnatinsa na cire tallafin man fetur inda ya bayyana shawarar daya daga cikin abokan hamayyarsa ta siyasa ta son dawo da tsarin a matsayin “alamar rashin sanin ya kamata sosai game da harkokin mulki da tattalin arziki.”
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da ya karbi bakuncin Gwamnan Jihar Osun Ademola Adeleke—wanda aka sake zaba—a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.s
Yayin da yake sharhi kan yanayin tattalin arzikin kasar Shugaban ya ce: “Na ga daya daga cikin abokan hamayyara yana cewa zai dawo da tsarin tallafin man fetur. Na karanta hakan. Wannan yana nuna rashin sanin ya kamata sosai game da harkokin mulki da tattalin arziki.”
KARANTA KUMA: Shugaba Tinubu na fadada ayyukan samar da ababen more rayuwa zuwa bayan manyan birane – Mataimakin Shugaban Kasa Shettima
Shugaba Tinubu ya tuna cewa kafin ya karbi ragamar mulki a shekarar 2023 jihohi 27 na fuskantar kalubale wajen biyan hakkokin ma’aikata da masu karbar fansho inda suka dogara ga Gwamnatin Tarayya domin samun tallafi.
“Kafin na zo nan jihohi 27 sun kasa biyan albashi balle ma a yi maganar hakkokin masu ritaya” in ji shi.
Yayin da yake magana kan Jihar Osun Shugaban ya tuna lokacin da ma’aikata ke karɓar rabin albashi inda ya jaddada muhimmancin jihohi su kasance suna da ƙarfin kuɗi don sauke nauyin da ke kansu.
“A jiharku na san wani mutum da ake yi wa lakabi da ‘Half Salary’ (Rabin Albashi). Suna zuwa wurin gwamnatin tarayya suna roƙo ba tare da ikon yin komai ba. Albashin da kuke biya shi ke ciyar da iyalai” in ji Shugaba Tinubu.
Ya kuma bayyana nauyin da ke kan gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomi inda ya yi nuni da cewa babban ɓangaren al’ummar ƙasar suna zaune ne a jihohi da kuma al’ummomin yankuna.
“Suna nan a matakin ƙananan hukumomi. Suna nan a jihohi. Ina ne wurin da jama’a suka fi yawa? Suna nan a jihohi. A ajiye Shugaban ƙasa a gefe. A ɗauki kowane mutum a matsayin talaka mai buƙatar ciyar da iyalinsa” in ji shi.
Ladan Nasidi.



