Liberia Za Ta Karɓi Mutane Har 1,200 Da Aka Kora

Hukumomin kasar Liberia sun bayyana a ranar Talata cewa kasar ta amince ta karbi mutane har su kai 1,200 da aka kora daga Amurka Wannan mataki wani bangare ne na kokarin gwamnatin Trump na dakile shige da fice ba bisa ka’ida ba.
Za a ci gaba da dawo da wadannan mutane zuwa Liberia a tsawon shekara guda. Ana sa ran rukunin farko mai mutane 20 zai isa kasar a ranar Alhamis kamar yadda Ministan Yada Labarai na Liberia Jerolinmek Piah ya shaida wa manema labarai a birnin Monrovia.
KARANTA KUMA: Liberia ta sake jaddada alakar kasuwanci da zuba jari da Najeriya
Piah ya ce mutanen da ake turowa zuwa Liberia din na iya hadawa da ‘yan kasashen Afirka da sauran kasashen Yamma wadanda aka tantance lafiyarsu kuma aka tabbatar sun cancanci yin tafiya.
Gwamnatin Trump ta cimma irin wannan yarjejeniya da wasu ƙasashen Afirka don karɓar mutanen da aka kora daga Amurka waɗanda ba ‘yan ƙasar waɗannan ƙasashe ba ne.
Yarjejeniyar ta haifar da damuwa a tsakanin ƙungiyoyin kare haƙƙin ‘yan cirani musamman saboda wasu ‘yan cirani na iya samun umarnin kariya daga alkalan shige da fice na Amurka waɗanda ke hana a mayar da su ƙasashensu saboda damuwar tsaro.
Piah bai bayyana ko akwai wani daga cikin mutanen da ake sa ran isa Liberia da irin waɗannan umarnin kariya ba.
Ya ce waɗanda aka kora za su iya neman mafaka a Liberia bayan sun isa ko kuma su bar ƙasar duk lokacin da suka ga dama.
Liberiya za ta sami tallafi daga Amurka don gudanar da shirin da kuma ƙarfafa tsarin ƙaura in ji Piah.
AP/Ladan Nasidi



