Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Ta Kara Kaimi Wajen Tunkarar Cutar Ebola.

Hukumomin kiwon lafiya a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo sun kara kaimi wajen daukar matakan tinkarar cutar Ebola yayin da take ci gaba da yaduwa, inda jami’ai suka bayar da rahoton karuwar masu kamuwa da cutar a wasu yankuna da ta fi shafa sosai.
A ranar Laraba da ta gabata, Darakta Janar na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya gana da Shugaba Félix Tshisekedi a birnin Kinshasa; wannan shi ne karo na biyu da ya ziyarci kasar tun bayan sanar da barkewar cutar a tsakiyar watan Mayu.
Tedros, wanda Darakta Janar na Cibiyar Kula da Rigakafin Cututtuka ta Afirka (Africa CDC), Jean Kaseya, ya bayyana cewa lamarin na ci gaba da haifar da babban damuwa yayin da adadin masu kamuwa da cutar ke karuwa.
A cewar Ma’aikatar Lafiya ta Congo, an samu mutane 3,874 da aka tabbatar sun kamu da cutar, yayin da mutane 1,751 suka mutu sakamakon bullar ta.
KARANTA KUMA: WHO ta yi kira da a dauki matakan gaggawa kan cutar Ebola a DRC
Amurka ta sanar da samar da karin kudade na dala miliyan 242 domin ayyukan gaggawa na tinkarar Ebola, shiri don tunkarar cutar, da kuma tallafin jin kai a yankin baki daya.
Wannan annoba, wadda kwayar cutar *Bundibugyo* ke haifarwa, ita ce ta biyu mafi girma a tarihin bullar cutar Ebola, kuma ita ce mafi saurin yaduwa a tarihin kasar Congo. Kasancewar babu rigakafi ko magani da aka amince da shi na musamman ga wannan nau’in kwayar cutar, hukumomin kiwon lafiya na ta kokarin ganin sun shawo kan cutar tare da hana kara rasa rayuka.
Aisha.Yahaya , Lagos



