Hukumar INEC Ta Wallafa Takardun Cancantar ‘Yan Takara Ta Zaben 2027.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta wallafa bayanan sirri da takardun cancantar karatu da ‘yan takarar shugaban kasa da na Majalisar Dokoki ta Kasa daga jam’iyyun siyasa suka gabatar domin babban zaben shekarar 2027.
Bayanan, wadanda aka wallafa a shafin yanar gizo na hukumar, sun kunshi cancantar karatu na ‘yan takarar da sauran bayanai da ke cikin Fom na EC9, kamar yadda Dokar Zabe ta 2026 ta tanada.
KARANTA KUMA: INEC ta yi alkawarin cewa za a yi la’akari da kuri’u a zaben 2027
A cewar INEC, wannan mataki na wallafa bayanai ya zo daidai da jadawalin ayyukan da aka sabunta domin babban zaben 2027, kuma yana daga cikin takardun tsayawa takara da ‘yan takarar shugaban kasa da na Majalisar Dokoki ta Kasa suka gabatar domin fafatawa a zaben da aka tsara gudanarwa a ranar 16 ga watan Janairun 2027.
Hukumar ta kuma wallafa bayanan ‘yan takarar mataimakin shugaban kasa da jam’iyyun siyasa suka gabatar, tare da sanar da cewa za ta wallafa bayanan ‘yan takarar gwamna da na Majalisar Dokoki ta Jiha a ranar 29 ga watan Agostan 2026.
Sashe na 29(3) na Dokar Zabe ta 2026 ya tanadi wajibcin wallafa Fom na EC9 cikin kwana 21 bayan karbarsa daga jam’iyyun siyasa.
Aisha.Yahaya, Lagos



