Uganda Ta Sanar Da Kawo Karshen Bullar Cutar Ebola

A ranar Talata da ta gabata ne, Ministan Lafiya na Uganda, Chris Baryomunsi, ya ayyana cewa kasar ta kubuta daga cutar Ebola, bayan barkewar cutar mai haddasa zubar jini a kasar ta Gabashin Afirka, wadda ta kama mutane 20 tare da hallaka biyu daga cikinsu.
Mutane 15 cikin wadanda suka kamu da cutar a wannan karon—wadda aka sanar da barkewarta a tsakiyar watan Mayu—sun kamu da ita ne a makwabciyar kasar Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo; kasar da ta kasance cibiyar barkewar cutar, inda yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da ita ya zarce 3,000 a yanzu.
KARANTA KUMA: Ebola: Hukumar CDC ta Afirka na neman a dage dokar hana tafiye-tafiye zuwa Uganda
“A duk tsawon wannan lokaci, Ma’aikatar Lafiya ta ci gaba da sanya ido sosai a fadin kasar, kuma ba a sake samun wani sabon mutum da ya kamu da cutar Ebola ba,” in ji Ministan Lafiya, Chris Baryomunsi.
Reuters/Aisha.Yahaya, Lagos



